Ubangiji Zai Hukunta Duniya
1 Ubangiji zai hallaka duniya ya bar ta kufai. Zai kaɓantar da duniya ya watsar da jama’ar da take cikinta.
2 Bala’i ɗaya ne zai sami kowa da kowa, firistoci da sauran jama’a, bayi da iyayengijinsu, masu saye da masu sayarwa, masu ba da rance da masu karɓa, attajirai da matalauta.
3 Duniya za ta ragargaje ta zama kufai. Ubangiji ne ya faɗa, haka kuwa za a yi.
4 Duniya za ta bushe ta ƙeƙashe, duniya duka za ta raunana, duniya da sararin sama za su ruɓe.
5 Jama’ar sun ƙazantar da duniya da suka keta dokokin Allah, suka ta da alkawarin da ya yi don ya dawwama.
6 Saboda haka Allah ya aiko da la’ana ta hallaka duniya. Jama’arta suna karɓar sakayyar abin da suka aikata. ‘Yan kalilan ne suka ragu da rai.
7 Kurangun inabi sun bushe, ruwan inabi ya yi kaɗan. Dukan wanda yake farin ciki a dā, yanzu sai baƙin ciki yake yi,
8 kaɗe-kaɗen garayunsu da gangunansu na farin ciki sun ƙare.
9 Babu sauran waƙar farin ciki ga mashayan ruwan inabi, ba kuma wanda zai ƙara jin daɗin ɗanɗanar ruwan inabi.
10 A cikin birni kome ya birkice, an kulle kowane gida don a hana mutane shiga.
11 Mutane za su tsaya a tituna, suna ihu, suna neman ruwan inabi. Farin ciki ya ƙare har abada, ya ƙare a ƙasar.
12 Birnin ya zama kango, an farfashe ƙofofinsa.
13 Wannan shi ne abin da zai sami kowace al’umma ko’ina a duniya. Zai zama kamar ƙarshen kaka sa’ad da aka karkaɗe zaitun daga kowane itace, aka kuma gama tsinke ‘ya’yan inabi daga kurangar inabi.
14 Waɗanda suka tsira za su raira waƙa don farin ciki. Waɗanda suke wajen yamma za su ba da labarin girman Allah,
15 waɗanda suke wajen gabas kuma za su yabe shi. Jama’ar da take zaune a gefen teku za su yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila.
16 Daga manisantan wurare na duniya za mu ji waƙoƙin yabon Isra’ila, al’umma adala.
Amma ba ni da sauran sa zuciya! Lalacewa nake yi! Maciya amana suna ta cin amana, cin amanarsu sai gaba gaba yake yi.
17 Ya jama’ar duniya, razana, da wushefe, da tarkuna suna jiranku.
18 Duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa daga razana zai fāɗa cikin wushefe, wanda kuma ya tsere daga wushefe za a kama shi a tarko. Za a kwararo ruwa daga sama kamar da bakin ƙwarya, harsashin ginin duniya zai jijjigu.
19 Duniya za ta tsage, ta farfashe ta wage.
20 Duniya kanta za ta yi tangaɗi kamar mashayi, ta yi ta yin lau kamar rumfa a lokacin hadiri. Nauyin zunuban duniya ya rinjaye ta har ƙasa, za ta fāɗi, ba za ta ƙara tashi ba.
21 A wannan rana Ubangiji zai hukunta wa ikoki na sama, da sarakunan da suke a duniya.
22 Allah zai tattara sarakuna wuri ɗaya kamar ɗaurarru a rami, zai kulle su a kurkuku kafin lokacin da zai hukunta su ya yi.
23 Wata zai duhunta, rana ba za ta ƙara haskakawa ba, domin Ubangiji Mai Runduna yake sarauta. Zai yi mulki a Urushalima a kan Dutsen Sihiyona, shugabannin jama’a za su dubi ɗaukakarsa.