Faɗakarwa game da Ifraimu
1 Mulkin Isra’ila ya ƙare, darajarsa tana dushewa kamar rawanin furanni a kan shugabanninsa da suka bugu da giya. Sun bulbula turare a kawunansu na girmankai, amma ga su nan a kwance bugaggu.
2 Ubangiji yana da wani ƙaƙƙarfa mai iko a shirye don ya fāɗa musu da yaƙi. Zai zo kamar hadirin ƙanƙara, kamar kwararowar ruwan sama, kamar kuma rigyawa mai kirmewa wadda ta shafe ƙasa.
3 Za a tattake girmankan bugaggun shugabannin nan.
4 Darajan nan mai dushewa ta shugabanni masu girmankai za ta shuɗe kamar ‘ya’yan ɓaure, nunan fari, da aka tsinke aka cinye nan da nan da nunarsu.
5 Rana tana zuwa da Ubangiji Mai Runduna zai zama kamar rawanin furanni mai daraja ga jama’arsa da suka ragu.
6 Zai ba da ruhun adalci ga waɗanda suke alƙalai, ƙarfin hali kuma ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofin birni.
Faɗaka da Alkawari ga Urushalima
7 Har da annabawa da firistoci, tangaɗi suke yi, mashaya ne. Sun sha ruwan inabi da barasa da yawa, suna ta tuntuɓe barkatai. Annabawan sun bugu ƙwarai, har ba su iya fahimtar wahayin da Allah ya aiko musu ba, firistoci su ma sun bugu, har sun kāsa yanke shari’un da aka kawo musu.
8 Duk sun cika teburorin da suke zaune da amai, ba inda ba su amaye ba.
9 Suna gunaguni a kaina suna cewa, “Su wa wannan mutum yake tsammani yana koya musu? Wa yake bukatar jawabinsa? Sai ga ‘yan yaran da aka yaye kaɗai yake da amfani!
10 Yana ƙoƙari ya koya mana baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi.”
11 Idan ba za ku saurare ni ba, to, Allah zai yi amfani da baƙi masu magana da harshen da ba ku sani ba, su koya muku darasi.
12 Ya miƙa muku hutawa da wartsakewa, amma kun ƙi saurarawa gare shi.
13 Saboda haka ne Ubangiji zai koya muku baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi. Sa’an nan kowane ɗaga ƙafar da kuka yi, za ku yi tuntuɓe, za a yi muku rauni, a kama ku a tarko, a kai ku kurkuku.
14 Yanzu fa ku mutane masu girmankai, da kuke mulki a nan a Urushalima a kan wannan jama’a, ku saurara ga abin da Ubangiji yake faɗa.
15 Kuna fāriya a kan alkawarin da kuka yi da mutuwa, kun ƙulla yarjejeniya da lahira. Kun tabbata masifa za ta ƙetare ku sa’ad da ta zo, domin kun dogara ga ƙarairayi da ruɗi don su kiyaye ku.
16 Yanzu fa ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan kafa ƙaƙƙarfan harsashin gini a Sihiyona. A kansa zan sa ƙaƙƙarfan dutsen kusurwa. A kansa an rubuta wannan magana, ‘Amincin da yake kafaffe mai haƙuri ne kuma.’
17 Adalci ne zai zama igiyar gwajin tushen ginin, aminci kuma zai zama shacin dirin ginin.
Hadirin ƙanƙara zai share dukan ƙarairayin da kuke dogara gare su, rigyawa za ta hallakar da zaman lafiyarku.”
18 Alkawarin da kuka ƙulla da mutuwa ya tashi, yarjejeniyar da kuka yi da lahira, an soke ta. Sa’ad da masifa ta auko za a hallaka ku.
19 Za ta yi ta auko muku a kai a kai kowace safiya. Tilas ku sha ta dare da rana. Kowane sabon jawabin da zai zo muku daga wurin Allah, zai kawo muku sabuwar razana!
20 Za ku zama kamar mutumin da ya zama abin karin magana, wanda ya yi ƙoƙari ya kwanta a gajeren gado, ya kuma rufa da ɗan siririn bargo.
21 Ubangiji zai yi yaƙi kamar yadda ya yi a Dutsen Ferazim da a Kwarin Gibeyon domin ya aikata abin da ya yi nufin yi, ko da yake ayyukansa suna da ban al’ajabi. Zai gama aikinsa, wannan aiki kuwa mai ban al’ajabi ne.
22 Kada ku yi dariya saboda faɗakarwar da nake yi muku! Idan kuwa kun yi, zai ƙara yi muku wuya ku tsira. Na ji niyyar da Ubangiji Mai Runduna ya yi, ta ya hallaka dukan ƙasar.
Hikimar Allah
23 Ku kasa kunne ga abin da nake cewa, ku mai da hankali ga abin da nake faɗa muku.
24 Manomi ba zai dinga huɗar gonakinsa har abada ba, ya yi ta shirya su domin shuka.
25 Da zarar ya shirya ƙasar yakan shusshuka ganyayen ci, kamar su kanumfari da ɗaɗɗoya, yakan kuma dasa kunyoyin alkama da na sha’ir, a gyaffan gonakin kuwa yakan shuka hatsi.
26 Ya san yadda zai yi aikinsa, gama Allah ya koya masa.
27 Ba ya bugun kanumfari da ɗaɗɗoya da ƙaton kulki, a maimakon haka yakan yi da ‘yan sanduna sirara.
28 Ba zai yi ta bugun alkama, har ya ɓata tsabar ba, ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba.
29 Dukan wannan hikima daga wurin Ubangiji Mai Runduna ne. Shirye-shiryen da Allah ya yi na hikima ne kullum kuwa sukan yi nasara!