Urushalima da Maƙiyanta
1 Bagaden Allah, Urushalima kanta, ƙaddara ta auko mata! Birnin da Dawuda ya kafa zango, ƙaddara ta auko mata! Bari shekara ɗaya ko biyu su zo su wuce suna shagulgulansu, suna bukukuwansu,
2 sa’an nan Allah zai kawo wa birnin wanda ake ce da shi, “Bagaden Allah,” masifa. Za a yi kuka a yi kururuwa, birnin kansa za a maishe shi bagade inda za a ƙona hadayun ƙonawa!
3 Allah zai tasar wa birnin, ya kewaye shi da yaƙi.
4 Urushalima za ta zama kamar fatalwar da take ƙoƙarin yin magana daga ƙarƙashin ƙasa, guni yana fitowa daga turɓaya.
5 Ya Urushalima, dukan baƙin da suka auka miki da yaƙi za a hure su kamar yadda iska take hure ƙura, sojojinsu kuma masu firgitarwa za a hure su kamar yadda iska take hure tattaka. Farat ɗaya ba zato ba tsammani,
6 Ubangiji Mai Runduna zai cece ki da tsawar hadiri da girgizar ƙasa. Zai aiko da hadirin iska da gagarumar wuta.
7 Sa’an nan dukan sojojin sauran al’umman da suka fāɗa wa birni inda bagaden Allah yake da yaƙi, da dukan makamansu, da kayayyakin yaƙinsu, kome da kome za su shuɗe kamar mafarki, kamar tunanin dare.
8 Dukan al’ummai da suka tattaru don su yaƙi Urushalima, za su zama kamar mutum mayunwaci da ya yi mafarki yana cin abinci, ya farka yana a mayunwacinsa, kamar wanda yake mutuwa da ƙishi ya yi mafarki yana kwankwaɗar ruwa, ya farka da busasshen maƙogwaro.
Makantar Isra’ilawa da Riyarsu
9 Ku ci gaba da aikin wautarku! Ku ci gaba da makancewarku, ku yi ta zama a makance. Ku bugu ba tare da kun sha ruwan inabi ba! Ku yi ta tangaɗi, ba don kun sha ko ɗigon ruwan inabi ba!
10 Ubangiji ya sa ku ku yi gyangyaɗi ku yi barci mai nauyi. Annabawa ne ya kamata su zama idon jama’a, amma Allah ya rufe idanunsu.
11 Za a ɓoye muku ma’anar kowane annabci na cikin wahayi. Zai zama kamar naɗaɗɗen littafin da aka liƙe. Ko kun kai wa wanda ya iya karatu, don ya karanta muku, zai ce ba zai iya ba saboda a liƙe yake.
12 In kuwa kun ba wanda bai iya karatu ba, kuka roƙe shi ya karanta muku, zai ce bai iya karatu ba.
13 Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun ce suna mini sujada, amma kalmominsu ba su da ma’ana, zukatansu kuma suna wani wuri dabam. Addininsu ba wani abu ba ne, sai dai dokoki ne da ka’idodin mutane da suka haddace.
14 Don haka zan firgita su ba zato ba tsammani, da dūka a kai a kai. Waɗanda suke da hikima za su zama wawaye, dukan wayon nan nasu kuwa ba zai amfana musu kome ba.”
Maƙaryatan Mashawarta
15 Waɗanda suke ƙoƙarin ɓoye wa Ubangiji shirye-shiryensu sun shiga uku! Suna gudanar da dabarunsu a ɓoye, suna tsammani ba wanda zai gan su ko ya san abin da suke yi.
16 Sun birkitar da kome! Wane ne ya fi muhimmanci, mai ginin tukwane ko yumɓun? Abin da mutum ya yi da hannunsa ya iya ce wa mutumin, “Ba kai ka yi ni ba”? Ko kuma zai iya ce masa, “Ai, ba ka san abin da kake yi ba”?
Fansar Isra’ila
17 Kamar yadda karin maganar ta ce, kafin a jima kurmi zai zama gona, gona kuma za ta zama kurmi.
18 A wannan rana, kurame za su ji sa’ad da aka karanta littafi da murya, makafi kuwa waɗanda suke zaune cikin duhu za su buɗe idanunsu su gani.
19 Matalauta da masu tawali’u za su sāke samun farin ciki wanda Allah Mai Tsarki na Isra’ila ya bayar.
20 Zai zama ƙarshen waɗanda suke zaluntar waɗansu, suna raina Allah. Za a hallakar da kowane mai zunubi.
21 Allah zai hallakar da waɗanda suke zambatar waɗansu, da waɗanda sukan hana a hukunta wa masu mugun laifi, da waɗanda sukan yanka ƙarya don a hana wa amintattu samun shari’ar adalci.
22 Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya fanshi Ibrahim daga wahala, ya ce, “Jama’ata, ba za a ƙara kunyatar da ku ba, fuskokinku ba za su ƙara yanƙwanewa don kunya ba.
23 Za ku ga ‘ya’yan da zan ba ku, sa’an nan ne za ku tabbatar, cewa ni ne Allah Mai Tsarki na Isra’ila. Za ku girmama ni, ku yi tsorona.
24 Wawaye za su koya su gane, waɗanda a kullum sai gunaguni suke yi, za su yi murna su koya.”