Hukuncin Ubangiji a kan Yahuza da Urushalima
1 Yanzu fa Ubangiji, Ubangiji Mai Runduna, yana gab da ya kwashe kowane abin da kowane mutum da jama’ar Urushalima da na Yahuza suke dogara da su. Zai kwashe abincinsu da ruwan shansu,
2 da jarumawansu, da sojojinsu, da alƙalansu, da annabawansu, da masu yi musu duba, da manyan mutanensu,
3 da shugabannin sojojinsu, da na farar hula, da ‘yan siyasarsu, da kowane mai aikin sihiri don ya sarrafa abubuwan da yake faruwa.
4 Ubangiji zai sa yaran da ba su balaga ba su mallaki jama’ar.
5 Za a yi ta cutar juna. Matasa ba za su girmama manyansu ba, talakawa ba za su girmama na gaba da su ba.
6 Lokaci yana zuwa sa’ad da mutanen wani dangi za su zaɓi ɗaya daga cikinsu, su ce, “Kai da kake da ɗan abin sawa za ka zama shugabanmu a wannan lokaci na wahala.”
7 Amma zai amsa, ya ce, “Ba ni ba dai! Ba zan iya taimakonku ba. Ba ni ma da abinci sam, ko tufafi ma. Kada ku naɗa ni shugabanku!”
8 Hakika Urushalima ta shiga uku! Yahuza tana kan fāɗuwa! Duk abin da suke faɗa, da abin da suke yi, na gāba da Ubangiji ne, a fili suke raina Allah, shi kansa.
9 Ayyukansu na son zuciya za su zama shaida gāba da su. Suna ta aikata zunubi a fili, kamar yadda mutanen Saduma suka yi. Sun shiga uku, su ne kuwa suka jawo wa kansu.
10 Adalai za su yi murna, kome zai tafi musu daidai. Za su ji daɗin abin da suka aikata.
11 Amma mugaye sun shiga uku, za a sāka musu bisa ga abin da suka aikata.
12 Masu ba da rance da ruwa suna zaluntar jama’ata, masu ba da bashi kuwa suna cutarsu.
Ya jama’ata, shugabanninku a karkace suke bi da ku, saboda haka ba ku san inda za ku nufa ba.
Ubangiji Yana Hukunta Jama’arsa
13 Ubangiji a shirye yake ya hurta maganarsa, a shirye yake ya hukunta al’ummai.
14 Ubangiji ya kawo dattawa da shugabannin jama’arsa a gaban shari’a. Ga laifin da ya same su da shi, “Kun washe gonakin inabi, kun cika gidajenku da abin da kuka ƙwato daga matalauta.
15 Ba ku da izinin da za ku ragargaza jama’ata, ku cuci matalauta, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”
Hukunci a kan Matan Urushalima
16 Ubangiji ya ce, “Duba irin girmankai da matan Urushalima suke da shi! Suna tafe suna hura hanci, a koyaushe suna ta fara’a irin ta yaudara, suna takawa ɗaya ɗaya a hankali da mundaye a ƙafafunsu, suna cas cas.
17 Amma zan hukunta su, in aske kawunansu, in bar su ƙwal.”
18 Rana tana zuwa sa’ad da Ubangiji zai raba matan Urushalima da dukan abin da suke taƙama da shi, da kayan adon da suke sawa a ƙafafunsu, da kawunansu, da wuyansu,
19 da hannuwansu. Zai raba su da lulluɓinsu,
20 da hulunansu. Zai raba su da layun da suke sa wa damatsansu, da kwankwasonsu,
21 da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu.
22 Ubangiji zai raba su da dukan kyawawan rigunansu na ado, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakunkunansu,
23 da rigunansu na yanga, da ƙyallayensu na lilin, da adikai, da gyale masu tsawo waɗanda suke sawa a kawunansu.
24 Maimakon su riƙa ƙanshin turare, za su yi wari, a maimakon abin ɗamara, za su yi ɗamara da igiyoyi masu kaushi, a maimakon su kasance da kyakkyawan gashi, za su zama masu sanƙo, a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki, kyansu zai zama abin kunya!
25 Jama’ar garin, i, har da ƙarfafan mutane, za a kashe su a yaƙi.
26 Ƙofofin birnin za su yi makoki, su yi kuka.
Za a kamanta birnin da matar da take zaune a ƙasa tsirara.