Jawabin Ubangiji na Ta’aziyya ga Isra’ila
1 Ubangiji ya ce,
“Ka ta’azantar da jama’ata.
Ka ta’azantar da su!
2 Ka ƙarfafa jama’ar Urushalima.
Ka faɗa musu sun sha wahala, ta isa,
Yanzu kuwa an gafarta musu zunubansu.
Na yi musu cikakken hukunci saboda dukan zunubansu.”
3 Murya tana kira tana cewa,
“Ka shirya hanya a jeji domin Ubangiji!
Ka share hanya a hamada domin Allahnmu!
4 Za a cike kowane kwari,
Za a baje kowane dutse.
Tuddai za su zama fili,
Ƙasa mai kururrumai za ta zama sumul.
5 Sa’an nan za a bayyana ɗaukakar Ubangiji,
Dukan ‘yan adam kuwa za su gan ta.
Ubangiji ne kansa ya yi wannan alkawari.”
6 Murya ta yi kira ta ce, “Ka yi shela!”
Na yi tambaya na ce, “Shelar me zan yi?”
“Ka yi shela, cewa dukan ‘yan adam kamar ciyawa suke,
Ba su fi furannin jeji tsawon rai ba.
7 Ciyawa takan bushe, furanni kuma sukan yi yaushi
Sa’ad da Ubangiji ya aiko da iska ta hura ta kansu.
Mutane kuwa ba su fi ciyawa ƙarfi ba!
8 Hakika ciyawa takan bushe, furanni kuwa su yi yaushi,
Amma maganar Allah ba za ta taɓa faɗuwa ba!”
9 Ki haura a kan dutse mai tsayi, ke Urushalima,
Ki faɗi albishir!
Ki yi kira da babbar murya, ya Sihiyona,
Ki faɗi albishir!
Yi magana da ƙarfi, kada kuwa ki ji tsoro.
Ki faɗa wa garuruwan Yahuza,
Cewa Allahnsu yana zuwa!
10 Ubangiji yana zuwa ya yi mulki da iko,
Zai taho tare da mutanen da ya cece su.
Ga shi, zai kawo lada
Zai kuma yi wa mutane sakamako.
11 Zai lura da garkensa kamar yadda makiyayi suke yi,
Zai tattara ‘yan raguna wuri ɗaya,
Zai ɗauke su ya rungume su,
A hankali zai bi da iyayensu.
Allah na Isra’ila, Gagara Misali
12 Akwai wanda zai iya auna teku da tafin hannu,
Ko sararin sama da tafin hannunsa?
Akwai wanda zai iya tallabe turɓayar duniya a cikin finjali,
Ko ya iya auna duwatsu da tuddai a ma’auni?
13 Akwai wanda zai iya umartar Ubangiji ya yi abu?
Wa zai iya koya wa Ubangiji, ko ya yi masa shawara?
14 Da wa Allah yake yin shawara
Domin ya sani, ya kuma fahimta,
Ya kuma koyi yadda za a yi abubuwa?
15 Al’ummai ba kome ba ne a wurin Ubangiji,
Ba su fi ɗigon ruwa ba,
Manisantan tsibirai ba su fi ƙura nauyi ba.
16 Dukan dabbobin da yake a jejin Lebanon
Ba su isa hadaya guda ga Allahnmu ba,
Itatuwan jejin kuma ba su isa a hura wuta da su ba.
17 Al’ummai ba kome ba ne ko kaɗan a gare shi.
18 Da wa za a iya kwatanta Allah?
Wa zai iya faɗar yadda yake?
19 Shi ba kamar gunki yake ba, wanda mutane suka yi,
Maƙera kuma suka dalaye da zinariya,
Suka sa shi cikin abin da suka yi da azurfa.
20 Mutum wanda bai isa samun azurfa ko zinariya ba,
Yakan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba.
Yana neman gwanin sassaƙa
Domin ya yi masa siffa wadda ba za ta fāɗi ba.
21 Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba?
Ashe, ba a faɗa maka ba tuntuni?
Ashe, ba ka ji yadda aka fara duniya ba?
22 Wanda yake zaune a kursiyi ne ya yi ta,
Can ƙwanƙolin duniya, gaba kuma da sararin sama,
Yana ganin mutane a ƙarƙas kamar ‘yan ƙananan ƙwari.
Ya miƙa sararin sama kamar labule,
Kamar kuma alfarwa domin mutane su zauna ciki.
23 Yakan kawo masu mulki masu iko ƙwarai,
Ya kuwa mai da su ba kome ba ne,
24 Suna kama da ƙaramin dashe
Wanda bai daɗe ba,
Bai yi ko saiwar kirki ba.
Sa’ad da Ubangiji ya aiko da iska,
Sai su bushe, iskar ta hure su kamar ƙaiƙayi.
25 Da wane ne za a kwatanta Allah Mai Tsarki?
Ko akwai wani mai kama da shi?
26 Ka dubi sararin sama a bisa!
Wane ne ya halicci taurarin da kake gani?
Shi wanda yake musu jagora kamar sojoji,
Ya sani ko su guda nawa ne,
Yana kiran dukansu, ko wanne da sunansa!
Ikonsa da girma yake,
Ba a taɓa rasa ko ɗayansu ba!
27 Isra’ila, me ya sa kake gunaguni,
Cewa Ubangiji bai san wahalarka ba,
Ko ya kula ya daidaita abubuwa dominka?
28 Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba?
Ubangiji Madawwamin Allah ne?
Ya halicci dukkan duniya.
Bai taɓa jin gajiya ko kasala ba.
Ba wanda ya taɓa fahimtar tunaninsa.
29 Yakan ƙarfafa masu kasala da masu jin gajiya.
30 Har da waɗanda suke yara ma, sukan ji kasala,
Samari sukan siƙe su fāɗi,
31 Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako
Za su ji an sabunta ƙarfinsu.
Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa,
Sa’ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba,
Sa’ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.