Bawan Ubangiji
1 Ubangiji ya ce,
“Ga bawana, wanda na ƙarfafa,
Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa.
Na cika shi da ikona,
Zai kuwa kawo shari’ar gaskiya ga dukan al’ummai.
2 Ba zai yi tsawa ko ya ta da muryarsa ba,
Ko ya yi jawabi da babbar murya a tituna.
3 Zai lallaɓi marasa ƙarfi,
Ya nuna alheri ga tafkakku.
Zai kawo madawwamiyar gaskiya ga duka.
4 Ba zai fid da zuciya ko ya karai ba,
Zai kuma kafa gaskiya a duniya,
Manisantan ƙasashe sun zaƙu, suna jiran koyarwarsa.”
5 Allah ya halicci sammai ya kuma shimfiɗa su,
Ya yi duniya, da dukan masu rai nata,
Ya ba da rai da numfashi ga dukan mutanenta.
Yanzu kuwa Ubangiji Allah ya ce wa bawansa,
6 “Ni Ubangiji, na kira ka, na kuma ba ka iko
Domin ka ga ana aikata gaskiya a duniya.
Ta wurinka zan yi wa dukan mutane alkawari,
Ta wurinka zan kawo haske ga al’ummai.
7 Za ka buɗe idanun makafi,
Ka kuma kwance waɗanda suke ɗaure a kurkuku masu duhu.
8 “Ni kaɗai ne Ubangiji Allahnka.
Ba wani allahn da zai sami ɗaukakata,
Ba zan bar gumaka su sami yabona ba.
9 Abubuwan da na faɗa yanzu sun cika.
Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwa,
Tun kafin ma su soma faruwa.”
Yabo ga Ubangiji domin Cetonsa
10 Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji,
Ku raira yabo ku dukan duniya!
Ku yabe shi, ku da kuke tafiya ta teku,
Ku yabe shi, ku dukan halitta a teku!
Ku raira, ku manisantan ƙasashe, da dukan waɗanda suke a can!
11 Bari hamada da garuruwanta su yabi Allah,
Bari mutanen Kedar su yabe shi!
Bari su da suke zaune a birnin Sela
Su yi sowa don murna daga ƙwanƙolin duwatsu!
12 Bari waɗanda suke a manisantan ƙasashe su yi yabo,
Su kuma girmama Ubangiji!
13 Ubangiji ya fita domin ya yi yaƙi kamar jarumi,
Ya shirya, ya kuma ƙosa domin yaƙi.
Ya yi gunzar yaƙi da tsawar yaƙi,
Ya nuna ikonsa a kan abokan gābansa.
Allah Ya Yi wa Mutanensa Alkawarin Taimako
14 Allah ya ce,
“Na daɗe na yi shiru,
Ban amsa wa jama’ata ba.
Amma yanzu lokaci ya yi da zan yi wani abu,
Na yi ƙara kamar matar da take fama da zafin naƙuda.
15 Zan lalatar da tuddai da duwatsu,
In kuma busar da ciyawa da itatuwa,
Zan mai da kwaruruka inda akwai rafi hamada,
In kuma busar da kududdufan ruwa.
16 “Zan yi wa mutanena makafi jagora
A hanyar da ba su taɓa bi ba.
Zan sa duhunsu ya zama haske,
In kuma sa ƙasa mai kururrumai ta zama sumul a gabansu.
Ba zan kasa yin waɗannan abu ba.
17 Dukan waɗanda suke dogara ga gumaka,
Masu kiran siffofi allolinsu,
Za a ƙasƙantar da su, su kuma sha kunya.”
Isra’ila Suka Kāsa Koyo
18 Ubangiji ya ce,
“Ku kasa kunne, ya ku kurame!
Ku duba da kyau sosai, ku makafi!
19 Akwai sauran wanda ya fi bawana makanta,
Ko wanda ya fi manzona kurunta, wato wanda na aiko?
20 Isra’ila, kun ga abu da yawa,
Amma bai zama da ma’ana a gare ku ba ko kaɗan.
Kuna da kunnuwan da za ku ji,
Amma a ainihi me kuka ji?”
21 Ubangiji shi Allah ne da ya ƙosa ya yi ceto saboda gaskiyarsa,
Saboda haka yana so a girmama koyarwarsa,
22 Amma yanzu an washe mutanensa,
Aka kukkulle su a kurkuku,
Aka ɓoye su a rami.
Aka yi musu fashi, aka washe su,
Ba wanda ya zo domin ya kuɓutar da su.
23 Ko akwai wanda zai kasa kunne ga wannan?
Ko za ku kasa kunne ku yi lura daga yanzu?
24 Wane ne ya ba da Isra’ila ga masu waso?
Ubangiji ne kansa, shi wanda muka yi wa zunubi!
Ba mu iya zama kamar yadda yake so mu yi ba,
Ko mu yi biyayya da koyarwarsa da ya ba mu.
25 Domin haka ya sa mu ji zafin fushinsa,
Mu kuma sha wahalar da yaƙi ya kawo.
Fushinsa ya yi ƙuna cikin dukan Isra’ila kamar wuta,
Amma ba mu taɓa sanin abin da yake faruwa ba,
Ba mu koyi kome daga wannan ba ko kaɗan.