1 “Wannan ne ƙarshen allolin Babila!
Dā ana yi wa Bel da Nebo sujada,
Amma yanzu ana labtunsu a kan jakuna,
Sun zama nawaya a kan dabbobin da suka gaji!
2 Wannan ne ƙarshen waɗannan alloli,
Gumaka ba su iya ceton kansu,
Aka kame su aka tafi da su.
3 “Ku kasa kunne gare ni ku zuriyar Yakubu,
Dukanku, mutanena da kuka ragu.
Ina ta lura da ku tun daga lokacin da aka haife ku.
4 Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku,
Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura.
Ni na halice ku zan kuwa lura da ku,
Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”
5 Ubangiji ya ce, “Da wane ne za ku kwatanta ni?
Akwai wani mai kama da ni?
6 Mutane suka buɗe alabensu suna zazzage zinariya,
Suna auna azurfa a kan ma’auni.
Suka yi jingar maƙerin zinariya don ya yi musu gunki,
Sa’an nan suka rusuna suka yi masa sujada!
7 Suka ɗauke shi a kafaɗunsu su tafi da shi,
Suna ajiyewa a wani wuri, ya yi ta tsayawa a can,
Ba ya iya motsawa daga inda yake.
Idan wani ya yi addu’a gare shi, ba zai iya amsawa ba,
Ko ya cece shi daga bala’i.
8 “Ku tuna da wannan, ku masu zunubi,
Ku dubi irin abin da na yi.
9 Ku tuna da abin da ya faru tuntuni,
Ku sani, ni kaɗai ne Allah,
Ba kuwa wani mai kama da ni.
10 Tun da farko na faɗa muku yadda abin zai zama,
Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru.
Na kuwa ce shirye-shiryena ba za su taɓa fāɗuwa ba,
Zan aikata dukan abin da na yi niyyar yi.
11 Ina kiran wani mutum ya zo daga gabas,
Zai kawo sura kamar shaho,
Zai kammala abin da na shirya.
Na yi faɗi, zai kuwa cika.
12 “Ku kasa kunne gare ni, ku mutane masu taurinkai,
Ku da kuke tsammani nasara tana can da nisa.
13 Ina kawo ranar nasara kusa,
Ba ta da nisa ko kaɗan.
Nasarata ba za ta yi jinkiri ba.
Zan ceci Urushalima,
Zan kuma kawo ɗaukaka ga Isra’ila a can.”