Bawan Ubangiji Zai Zama Haske ga Al’ummai
1 Ku kasa kunne gare ni, ku al’ummai manisanta,
Ku mutanen da suke zaune a can nesa!
Ubangiji ya zaɓe ni, tun kafin a haife ni,
Ya kuwa sa ni in zama bawansa.
2 Ya sa maganata ta yi kaifi kamar takobi,
Ya kiyaye ni da ikonsa.
Ya sa na zama kamar kibiya
Mai tsini shirayayyiya domin harbi.
3 Ya ce mini, “Isra’ila, kai bawana ne.
Mutane za su yabe ni saboda kai.”
4 Na ce, “Na yi aiki, amma a banza ne.
Na mori ƙarfina, amma ban ƙulla kome ba.”
Duk da haka na dogara ga Ubangiji, ya daidaita al’amura,
Shi zai sāka mini abin da na yi.
5 Ubangiji ya zaɓe ni tun kafin a haife ni.
Ya maishe ni bawansa domin in komo da mutanensa,
In komo da jama’ar Isra’ilan da aka warwatsar.
Ubangiji ya ba ni daraja,
Shi ne tushen ƙarfina.
6 Ubangiji ya ce mini,
“Bawana, ina da aiki mai girma dominka,
Ba komo da girman jama’ar Isra’ila da suka ragu kaɗai ba,
Amma zan sa ka zama haske ga al’ummai,
Domin dukan duniya ta tsira.”
7 Allah Mai Tsarki na Isra’ila, Mai Fansa,
Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai,
Al’ummai suka ƙi shi,
Bawa na masu mulki kuma,
“Sarakuna za su gan ka a sake,
Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma,
Shugabanni su kuma za su gani,
Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.”
Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji,
Allah Mai Tsarki na Isra’ila, ya zaɓi bawansa,
Ya kuwa cika alkawaransa.
Alkawarin Maido Urushalima
8 Ubangiji ya ce wa jama’arsa,
“Idan lokacin da zan cece ku ya yi, zan nuna muku alheri.
Zan ji kukanku in taimake ku.
Zan tsare ku in kiyaye ku,
Zan kuwa yi wa dukan mutane alkawari ta wurinku.
Zan bar ku ku sāke zama a ƙasarku wadda take kufai a yanzu.
9 Zan ce wa ‘yan kurkuku, ‘Ku tafi na sake ku!’
Waɗanda suke cikin duhu kuwa, in ce musu,
‘Ku fito zuwa wurin haske!’
Za su zama kamar tumakin da suke kiwo a tuddai,
10 Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba.
Ba za su sha zafin rana da na hamada ba,
Gama wanda yake ƙaunarsu ne zai bi da su.
Zai bi da su zuwa maɓuɓɓugan ruwa.
11 “Zan yi babbar hanya ta kan duwatsu,
In kuma shirya hanya domin mutanena su bi.
12 Mutanena za su zo daga can nesa,
Daga Birnin Sin a kudu,
Daga yamma, da arewa.”
13 Ku raira, ku sammai! Ki yi sowar murna, ke duniya!
Bari duwatsu su ɓarke da waƙa!
Ubangiji zai ta’azantar da mutanensa,
Zai ji juyayin mutanensa da suke shan wahala.
14 Amma mutanen Urushalima suka ce,
“Ubangiji ya yashe mu!
Ya manta da mu.”
15 Saboda haka Ubangiji ya amsa ya ce,
“Mace za ta iya mantawa da jaririnta,
Ta kuma ƙi ƙaunar ɗan da ta haifa?
Ya yiwu mace ta manta da ɗanta,
To, ni ba zan taɓa mantawa da ku ba.
16 Ya Urushalima, ba zan taɓa mantawa da ke ba,
Na rubuta sunanki a gabana.
17 “Su waɗanda za su sāke gina ki suna tafe yanzu,
Waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su tashi.
18 Ki dudduba, ki ɗaga idonki, ki ga abin da yake faruwa!
Mutanenki suna tattaruwa suna komowa gida!
Hakika, da yake ni ne Allah Mai Rai,
Za ki yi fāriya da mutanenki,
Kamar yadda amarya take fāriya da kayan adonta!
19 “Aka lalatar da ƙasar, ta zama kufai,
Amma yanzu za ta yi wa waɗanda suke komowa domin su zauna cikinta kaɗan.
Waɗanda suka lalatar da ke kuwa,
Za a kawar da su daga gare ki.
20 Mutanenki da aka haifa a lokacin zaman talala,
Wata rana za su ce miki,
‘Wannan ƙasa ta yi kaɗan ƙwarai,
Muna bukatar ƙarin wurin zama!’
21 Sa’an nan za ki ce wa kanki,
‘Wa ya haifa mini waɗannan ‘ya’ya?
Na rasa ‘ya’yana, ba kuwa zan iya haifar waɗansu ba.
Aka kore ni, aka yi mini ɗaurin talala,
Wane ne ya haifi waɗannan ‘ya’ya?
Aka bar ni, ni kaɗai,
Daga ina waɗannan ‘ya’ya suka fito?’ ”
22 Ubangiji Allah ya ce wa jama’arsa,
“Zan nuna alama ga al’ummai,
Za su kuwa kawo ‘ya’yanku gida.
23 Sarakuna za su zama kamar iyaye a gare ku,
Sarauniyoyi za su yi renonku kamar uwaye.
Za su rusuna har ƙasa su ba ku girma,
Da tawali’u za su nuna muku bangirma.
Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji,
Dukan mai jiran taimakon Ubangiji, ransa ba zai ɓaci ba.”
24 Kuna iya ku ƙwace wa sojoji wason da suka yi?
Kuna iya kuɓutar da ‘yan kurkuku daga ɗaurin masu baƙin mulki?
25 Ubangiji ya amsa ya ce,
“Wannan shi ne ainihin abin da zai faru.
Za a ƙwace kamammun yaƙi,
Za a kuma ƙwace wason da masu baƙin mulki ya yi.
Zan yi yaƙi da dukan wanda yake yaƙi da ku,
Zan kuwa kuɓutar da ‘ya’yanku.
26 Zan sa masu zaluntarku su karkashe juna,
Za su yi māye, da kisankai, da fushi.
Sa’an nan dukan ‘yan adam za su sani, ni ne Ubangiji,
Wanda ya cece ku, ya fanshe ku.
Za su sani ni ne Allah Mai Iko Dukka na Isra’ila.”