Waƙar Gonar Inabi
1 Ku saurara in raira muku wannan waƙa,
Waƙar abokina da gonar inabinsa.
Abokina yana da gonar inabi
A wani tudu mai dausayi.
2 Ya kauce ƙasar ya tsintsince duwatsun,
Ya daddasa itatuwan inabi mafi kyau.
Ya gina hasumiya don a yi tsaronsu,
Ya kuma haƙa rami inda za a matse ‘ya’yan inabin.
Ya yi ta jira don ‘ya’yan inabin su nuna,
Amma ko wannensu tsami take gare shi.
3 Saboda haka, abokina ya ce, “Ku jama’ar da yake zaune a Urushalima da Yahuza, ku shara’anta tsakanina da gonar inabina.
4 Akwai abin da ban yi mata ba? Me ya sa ta yi ‘ya’yan inabi masu tsami, maimakon ‘ya’yan inabi masu kyau da nake sa zuciya.
5 “Ga abin da zan yi wa gonar inabina. Zan cire shingen da yake kewaye da ita, in rushe bangon da ya kāre ta, in bar namomin jeji su cinye ta, su tattake ta.
6 Zan bar ciyayi su rufe ta. Ba zan yi wa kurangar inabin aski ba, ko in yi mata noma, amma zan bar sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa su rufe ta. Har ma zan sa gizagizai su hana ta ruwan sama.”
7 Isra’ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna,
Jama’ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa.
Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau,
Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai!
Ya zaci za su aikata abin da yake daidai,
Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!
Mugaye Sun Shiga Uku
8 Kun shiga uku! Kuna ƙara wa kanku gidaje da gonaki a kan waɗanda kuke da su a dā. Ba da jimawa ba za a ga ba sauran filin da zai ragu ga kowa, ku kaɗai za ku zauna a ƙasar.
9 Na ji Ubangiji Mai Runduna yana cewa, “Duk waɗannan manya manyan gidaje kyawawa za su zama kangwaye.
10 Kadada biyar na gonar inabi za ta ba da kwalaba shida kaɗai na ruwan inabi. Garwa ashirin na iri za su ba da tsabar hatsi garwa biyu!”
11 Kun shiga uku! Kukan tashi da sassafe ku fara sha, ku yi ta sha har yamma ta yi sosai, ku raba dare kuna buguwa.
12 A cikin bukukuwanku kuna kaɗa garaya, da bandiri, da bushe-bushe, da ruwan inabi. Amma ba ku gane da abin da Ubangiji yake yi ba.
13 Don haka za a kwashe ku, ku zama ‘yan sarƙa, a raba ku da ƙasarku. Yunwa za ta kashe shugabanninku, sauran jama’a kuwa ƙishirwa za ta kashe su.
14 Lahira ta ƙosa, ta wage bakinta. Ta lanƙwame manyan mutanen Urushalima da sauran babban taron jama’a masu hayaniya.
15 Za a kunyatar da kowa, dukan masu girmankai za a ƙasƙantar da su.
16 Amma Ubangiji Mai Runduna yana nuna girmansa ta wurin aikata abin da yake daidai, yana kuma bayyana shi Mai Tsarki ne, ta yadda yake shara’anta jama’arsa.
17 A cikin kangwayen birnin, raguna za su ci ciyawa, a nan ne kuma awaki za su sami wurin kiwo.
18 Kun shiga uku! Ba ku iya kuɓuta daga zunubanku ba.
19 Kukan ce, “Bari Ubangiji ya gaggauta ya aikata abin da ya ce zai yi don mu gani. Bari Allah, Mai Tsarki na Isra’ila, ya i da shirye-shiryensa. Bari mu ga abin da yake nufi.”
20 Kun shiga uku! Kun ce mugunta ita ce nagarta, nagarta kuwa mugunta. Kun mai da duhu shi ne haske, haske kuwa duhu. Kun mai da abin da yake mai ɗaci mai zaƙi, mai zaƙi kuwa kun maishe shi mai ɗaci.
21 Kun shiga uku! A tsammaninku ku masu hikima ne, masu wayo ƙwarai.
22 Kun shiga uku! Jarumawan kwalabar ruwan inabi! Masu ƙarfin zuciya marasa tsoro a gauraya shaye-shaye!
23 Amma kukan ƙyale masu laifi waɗanda suka ba ku rashawa, kukan kuwa ƙi yi wa marasa laifi shari’ar gaskiya.
24 Don haka, kamar yadda tattaka da busasshiyar ciyawa sukan yanƙwane su ƙone a wuta, saiwoyinku za su ruɓe, furanninku kuma za su bushe. Iska za ta kwashe su, domin kun ƙi abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah Mai Tsarki na Isra’ila, ya koya muku.
25 Ubangiji yana fushi da jama’arsa, ya miƙa hannunsa domin ya hukunta su. Duwatsu za su jijjigu, gawawwaki kuwa za a bar su a kan tituna kamar shara. Duk da haka Ubangiji ba zai huce daga fushinsa ba, ba kuwa zai janye hannunsa daga yin hukunci ba.
26 Ubangiji ya ba da alama a kirawo al’ummar da take nesa. Ya yi musu fīto su zo daga bangon duniya. Ga shi kuwa sun iso da sauri nan da nan.
27 Ko ɗaya ba wanda ya gaji, ba kuwa wanda ya yi tuntuɓe. Ba su yi gyangyaɗi ko barci ba. Ba abin ɗamarar da ya kwance, ba igiyar takalmin da ta tsinke.
28 Kibansu masu tsini ne, bakunansu kuwa a shirye suke don yin harbi. Kofaton dawakansu suna da ƙarfi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun karusansu kamar guguwa ne.
29 Sojojinsu na ruri kamar zakunan da suka kashe nama, suna kuwa ɗauke da shi don kada wani ya ƙwace musu.
30 Sa’ad da ranar ta yi, za su yi ruri a kan Isra’ila da ƙarfi kamar rurin teku. Ku duba ƙasan nan! Duhu da damuwa! Duhu ya haɗiye hasken.