Ƙaunar Ubangiji ga Isra’ila
1 Urushalima, kika zama kamar matar da ba ta da ɗa.
Amma yanzu kina iya rairawa, ki yi sowa saboda murna.
Yanzu za ki ƙara samun ‘ya’ya fiye da na
Matar da mijinta bai taɓa rabuwa da ita ba!
2 Ki fāɗaɗa alfarwar da kike zama ciki!
Ki ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta!
3 Za ki faɗaɗa kan iyakar ƙasarki a kowane gefe,
Jama’arki za su karɓi ƙasarsu
Wadda al’ummai suke mallaka yanzu,
Biranen da aka bari ba kowa, za su cika da mutane.
4 Kada ki ji tsoro, ba za a ƙara kunyatar da ke ba,
Ba kuwa za a ƙasƙantar da ke ba.
Za ki manta da rashin amincinki irin na matar ƙuruciya,
Za ki manta da matsanancin kaɗaicinki,
Mai kama da na gwauruwa.
5 Mahaliccinki zai zama kamar miji a gare ki,
Sunansa Ubangiji Mai Runduna!
Allah Mai Tsarki na Isra’ila mai fansarki ne,
Shi ne mai mulkin dukan duniya!
6 Kina kama da amarya
Wadda mijinta ya rabu da ita, tana baƙin ciki ƙwarai.
Amma Ubangiji yana kiranki zuwa gare shi, ya ce,
7 “A ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke,
Amma da ƙauna mai zurfi zan sāke karɓarki.
8 Na juya, na rabu da ke da fushi na ɗan lokaci,
Amma zan nuna miki ƙaunata har abada.”
Haka Ubangiji mai fansarki ya faɗa, shi wanda ya cece ki.
9 “Na yi alkawari a zamanin Nuhu,
Cewa ba zan ƙara rufe duniya da Ruwan Tsufana ba.
Yanzu kuwa ina miki alkawari,
Cewa ba zan ƙara yin fushi da ke ba,
Ba zan ƙara tsawata miki, ko in hukunta ki ba.
10 Duwatsu da tuddai za su ragargaje,
Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam.
Zan cika alkawarina na salama har abada.”
Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.
11 Ubangiji ya ce,
“Ya Urushalima, mai shan wahala, birnin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi,
Ba ki da wanda zai ta’azantar da ke.
Zan sake gina harsashinki da duwatsu masu daraja.
12 Zan gina hasumiyarki da jan yakutu,
Da ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske kamar hasken wuta,
Da garun da ya kewaye ki kuwa zan gina ta da lu’ulu’ai.
13 “Ni kaina zan koya wa mutanenki,
Zan kuwa ba su wadata da salama.
14 Adalci da gaskiya za su ƙarfafa ki.
Za ki tsira daga shan zalunci da razana.
Gama ba za su kusace ki ba.
15 Idan wani ya far miki,
Ya yi ne ba da yardata ba,
Dukan wanda ya hau ki da yaƙi zai fāɗi!
16 “Ni ne na halicci maƙeri
Wanda ya zuga wuta ya kuwa ƙera makamai.
Ni ne kuma na halicci mayaƙi
Wanda yakan mori makamai domin kisa.
17 Amma ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki,
Za ki iya amsa wa dukan waɗanda za su yi ƙararki.
Zan kāre bayina,
In kuwa ba su nasara.”
Ubangiji ne ya faɗa.