Allah Ya Kira Ishaya Ya Zama Annabi
1 A shekarar da sarki Azariya ya rasu na ga Ubangiji. Yana zaune a kursiyinsa a Sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika Haikali.
2 Kewaye da shi sai ga waɗansu talikai masu kama da harshen wuta a tsaye, ko wannensu yana da fikafikai shida. Ko wannensu ya rufe fuskarsa da fiffike biyu, jikinsa kuma da fiffike biyu, sauran fiffike biyu ɗin kuma, da su yake tashi.
3 Suna ta kiran junansu suna cewa,
“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki!
Ubangiji Mai Runduna Mai Tsarki ne!
Ɗaukakarsa ta cika duniya.”
4 Amon muryoyinsu ya sa harsashin ginin Haikali ya girgiɗa, Haikalin kansa kuma ya game da hayaƙi.
5 Sai na ce, “Sa zuciyata ya ƙare! Na shiga uku! Kowace maganar da ta fito bakina zunubi ce, ina zaune a tsakanin mutane waɗanda duk maganarsu zunubi ce, ba ta da tsarki. Amma yanzu da idona na ga Sarki, Ubangiji Mai Runduna!”
6 Sa’an nan ɗaya daga cikin talikan ya tashi ya sauko zuwa gare ni, yana riƙe da garwashin wuta wanda ya ɗauko da arautaki daga bagade.
7 Ya taɓa leɓunana da garwashin wutar ya ce, “Wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”
8 Sai na ji Ubangiji yana cewa, “Wa zan aika? Wa zai zama manzonmu?”
Sai na amsa na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”
9 Saboda haka sai ya ce mini in tafi in faɗa wa jama’a wannan jawabi cewa, “Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba. Kome yawan dubawar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.”
10 Sa’an nan ya ce mini, “Ka sa hankalin mutanen nan ya dushe, kunnuwansu su kurunce, idanunsu su makance, har da ba za su iya gani, ko ji, ko fahimta ba. In da za su yi haka mai yiwuwa ne su sāke juyowa gare ni in warkar da su.”
11 Na yi tambaya na ce, “Har yaushe zai ta zama haka, ya Ubangiji?”
Sai ya amsa, ya ce, “Har birane suka zama kufai ba kowa ciki. Har gidaje suka zama kangwaye. Har ƙasar kanta ta zama ba kowa, marar amfani.
12 Zan sa jama’a su tafi nesa, in sa ƙasar duka ta zama kango.
13 Ko da mutum ɗaya cikin goma zai ragu a ƙasar, shi ma za a hallaka shi. Zai zama kamar kututturen itacen oak wanda aka sare.”
Wato kututturen alama ce ta tohuwar jama’ar Allah zuwa gaba.