Haihuwar Sarkin Salama
1 Ba sauran baƙin ciki ga wadda take shan azaba. Dā an ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zabaluna da na Naftali, amma nan gaba wannan jiha za ta sami daraja, tun daga Bahar Maliya, zuwa gabashin ƙasar a wancan sashe na Urdun, har zuwa Galili kanta, wurin da baƙi suke zaune.
2 Jama’ar da suka yi tafiya cikin duhu,
Sun ga babban haske!
Suka zauna a inuwar mutuwa,
Amma yanzu haske ya haskaka su.
3 Ka ba su babbar murna, ya Ubangiji,
Ka sa su yi farin ciki.
Suna murna da abin da ka aikata,
Kamar yadda mutane suke murna sa’ad da suke girbin hatsi,
Ko sa’ad da suke raba ganima.
4 Gama ka karya karkiyar da ta nawaita musu,
Da kuma sandan da ake dukan kafaɗunsu da shi.
Kai ne, ya Ubangiji, ka kori al’ummar
Da ta zalunci jama’arka, ta kuma zambace su,
Daidai da yadda dā ka kori rundunar sojojin Madayana tuntuni.
5 Takalman sojojin da suka kawo yaƙi
Da dukan tufafinsu da suka birkiɗe da jini,
Za a ƙone su da wuta!
6 Ga shi, an haifa mana ɗa!
Mun sami yaro!
Shi zai zama Mai Mulkinmu.
Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al’ajabi,”
“Allah Maɗaukaki,”
“Uba Madawwami,”
“Sarkin Salama.”
7 Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba,
Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin,
Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa,
Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,
Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.
Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
Ubangiji Ya Yi Fushi da Isra’ila
8 Ubangiji ya hurta hukunci a kan mulkin Isra’ila, da a kan zuriyar Yakubu.
9 Dukan jama’ar Isra’ila, duk wanda yake zaune a birnin Samariya, zai sani Ubangiji ne ya aikata haka. Yanzu suna da girmankai suna fāriya. Sun ce,
10 “Gine-ginen da aka yi da tubali sun rushe, amma za mu sāke gina su da dutse. An sassare ginshiƙan da aka yi da itacen durumi, amma za mu sāke kakkafa su da kyawawan itatuwan al’ul.”
11 Ubangiji ya kuta maƙiyansu daga Rezin su fāɗa su da yaƙi.
12 Suriya daga gabas, da Filistiya daga yamma, sun wage bakinsu don su haɗiye Isra’ila. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.
13 Jama’ar Isra’ila ba su tuba ba, ko da yake Ubangiji Mai Runduna ya hukunta su, duk da haka ba su juyo ba.
14 A rana ɗaya Ubangiji zai hukunta shugabannin Isra’ila da jama’arta. Zai hallaka kawunansu da ƙafafunsu, da dabino da iwa,
15 wato tsofaffi da manyan mutane su ne kawunan, ƙafafu kuwa su ne annabawan da suke koyar da ƙarairayi!
16 Su waɗanda suke bi da jama’an nan, sun bashe su, sun ruɗar da su ɗungum.
17 Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.
18 Muguntar jama’a tana ci kamar wutar da take cinye ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya. Tana ci kamar wutar dawa wadda hayaƙinta take murtukewa har sama.
19 Saboda Ubangiji Mai Runduna ya yi fushi, hukuncinsa yana ci kamar wuta ko’ina a ƙasar, yana hallakar da jama’a, kowa na ta kansa.
20 A ko’ina a ƙasar jama’a sukan wawashe su ci ɗan abincin da suke iya samu, amma ba su taɓa ƙoshi ba. Har ‘ya’yansu ma suke ci!
21 Jama’ar Manassa da jama’ar Ifraimu suna fāɗa wa juna, tare kuma suke fāɗa wa Yahuza. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.