Adali da Mugu Dabam Suke
1 Karin maganar Sulemanu ke nan. Ɗa mai hikima abin fāriya ne ga mahaifinsa, amma wawa yakan jawo wa mahaifiyarsa baƙin ciki.
2 Abin da ka samu ta hanyar zamba ba zai yi albarka ba, amma gaskiya za ta cece ka.
3 Ubangiji ba zai bar mutumin kirki da yunwa ba, amma zai hana mugu ya kai ga biyan bukatarsa.
4 Ragwanci zai sa talauci, amma yin aiki sosai zai arzuta ka.
5 Mutum mai hankali yakan tattara amfanin gona da kaka, amma abin kunya ne a yi barci a lokacin girbi.
6 Mutumin kirki yakan karɓi albarka, maganganun mugun kuwa sukan ɓoye mugun halinsa.
7 Tunawa da mutumin kirki albarka ce, amma nan da nan za a manta da mugaye.
8 Mutane masu hankali sukan bi shawarar kirki, masu maganar wauta kuwa za su lalace.
9 Amintaccen mutum zai zauna lafiya ba abin da zai same shi, amma marasa aminci za a kama su.
10 Mutumin da ya ƙi faɗar gaskiya yana haddasa wahala, amma wanda ya bayyana gaskiya zai kawo salama.
11 Kalmomin mutumin kirki maɓuɓɓugan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.
12 Ƙiyayya takan haddasa wahala, amma ƙauna takan ƙyale dukan laifofi.
13 Mutane masu fasaha sukan yi magana mai ma’ana, amma wawaye suna bukatar horo.
14 Mutane masu hikima sukan nemi ilimi iyakar iyawarsu, amma sa’ad da wawa ya yi magana, wahala tana kusa.
15 Wadata takan kiyaye attajiri, amma tsiya takan hallaka matalauci.
16 Sakayyar da za a yi wa mutumin kirki ta rai ce, amma zunubi yakan sa a ƙara yin wani zunubi.
17 Mutumin da yake kasa kunne sa’ad da ake kwaɓarsa zai rayu, amma duk wanda bai yarda da kuskurensa ba yana cikin hatsari.
18 Mutumin da yake faɗar ƙarairayi maƙiyi ne, dukan wanda yake baza jitajita wawa ne.
19 Bisa ga yawan surutunka, mai yiwuwa ne ƙwarai ka yi zunubi, amma idan kai mai la’akari ne, sai ka yi shiru.
20 Kalmomin mutumin kirki suna kama da azurfa tsantsa, amma shawarwarin mugu ba su da wani amfani.
21 Kalmomin mutumin kirki za su amfani mutane da yawa, amma kana iya hallaka kanka da wauta.
22 Albarkar Ubangiji takan arzuta mutum, amma yawan aiki ba shi yake kawo arziki ba.
23 Wawa ne yake jin daɗin aikata mugunta, amma mai fasaha yana jin daɗin hikima.
24 Abin da mugun yake tsoro, shi yakan auko masa, amma adali yakan sami biyan bukatarsa.
25 Hadiri yakan taso ya wargaza mugaye, amma amintattu lafiya lau suke a ko yaushe.
26 Sam, kada ka sa malalaci ya yi maka wani abu, zai sa ka ka yi fushi, idanunka su cika da hawaye mai zafi.
27 Ka yi tsoron Ubangiji za ka rayu, ka yi tsawon rai, amma mugaye sukan mutu tun kwanansu bai ƙare ba.
28 Abin da mutanen kirki suke sa zuciya yakan kai su ga murna, amma mugaye ba su da wani abu da za su sa zuciya a kai.
29 Ubangiji yana kiyaye marasa laifi, amma yakan hallaka masu mugunta.
30 Kullayaumi adalai sukan yi zamansu lafiya, amma mugaye ba za su zauna a ƙasar ba.
31 Maganar adalai ta hikima ce, amma harshen da yake hurta mugunta, za a dakatar da shi.
32 Adalai sun san irin maganar da ta cancanta su faɗa, amma mugaye, kullum sukan faɗi maganar da za ta cutar.