Karin Magana Zancen Zaman Mutum
1 Mutane sun iya yin shirye-shiryensu, amma cikawa ta Ubangiji ce.
2 Za ka yi tsammani kowane abu da ka yi daidai ne, amma Ubangiji yana auna manufarka.
3 Ka roƙi Ubangiji, ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su.
4 Kowane abu da Ubangiji ya yi yana da makoma, makomar mugun kuwa hallaka ce.
5 Ubangiji yana ƙin kowane mutum da yake fariya. Irin wannan mutum ba zai kuɓuta daga hukunci ba.
6 Ka zama mai biyayya da aminci, Allah kuwa zai gafarta maka zunubinka. Ka dogara ga Ubangiji, ba wani mugun abu da zai same ka.
7 Lokacin da ka yi abin da Ubangiji yake so, ka iya mai da maƙiyanka su zama abokai.
8 Gara ka sami kaɗan ta hanyar gaskiya, da ka tara abu mai yawa ta hanyar zamba.
9 Kana iya yin shirye-shiryenka, amma Allah ne yake bi da kai cikin ayyukanka.
10 Sarkin da yakan yi magana ta wurin ikon Allah, a ko yaushe yakan yanke shawarar da yake daidai.
11 Ubangiji yana son ma’aunai su zama na gaskiya, kowane abin sayarwa kuma ya zama daidai.
12 Sarakuna ba za su iya jurewa da mugunta ba, gama adalci yake sa hukuma ta yi ƙarfi.
13 Sarki yana so ya ji gaskiya, zai kuwa ƙaunaci mutanen da suke faɗar gaskiya.
14 Mutum mai hikima yakan yi ƙoƙari ya faranta zuciyar sarki. Idan kuwa sarki ya hasala mai yiwuwa ne a kashe wani.
15 Alherin sarki kamar gizagizai ne masu kawo ruwan sama a lokacin bazara, akwai rai a ciki.
16 Yana da kyau, ya kuma fi kyau a sami hikima da ilimi fiye da zinariya da azurfa.
17 Mutumin kirki yana tafiya a hanyar da ta kauce wa mugunta, saboda haka ka kula da inda kake tafiya, za ta ceci ranka.
18 Girmankai jagora ne zuwa ga hallaka, fāriya kuwa zuwa ga fāɗuwa.
19 Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu tawali’u, da ka zama ɗaya daga cikin masu girmankai, har da za ka sami rabo daga cikin ganimarsu.
20 Ka mai da hankali ga abin da aka koya maka, za ka yi nasara. Ka dogara ga Ubangiji, za ka yi farin ciki.
21 Mutum mai hikima, wanda ya isa mutum, akan san shi ta wurin haziƙancinsa, kamar yadda kalmominsa suke da daɗi, haka ma rinjayarsa take.
22 Hikima maɓuɓɓugar rai ce ga mai hikima, amma ɓata lokaci ne a yi ƙoƙarin koya wa dakikai.
23 Mai hikima yakan yi tunani kafin ya yi magana, abin da ya faɗa yakan yi rinjaye ƙwarai.
24 Kalmomi masu daɗi suna kama da zuma, suna da daɗin ɗanɗana, suna kuma da amfani domin lafiyarka.
25 Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.
26 Marmarin cin abinci yakan sa ɗan ƙodago ya yi aiki da ƙwazo, domin yana so ya ci ya ƙoshi.
27 Mutumin da yake jin daɗin yin mugunta yakan tafi yawon nemanta, mugayen maganganunsa ƙuna suke kamar wuta.
28 Mugaye sukan baza jita-jita, suna zuga tashin hankali, suna raba aminai.
29 Mutum mai ta da zaune tsaye yakan ruɗi abokansa, ya kai su ga bala’i.
30 Ka kula da mutane masu murguɗa baki suna kaɗa gira a kanka, sun yi tunanin wani mugun abu ke nan.
31 Furfurar tsufa rawanin daraja ce, sakamako ne ga ran mai adalci.
32 Ya fi kyau ka zama mai haƙuri da ka zama mai ƙarfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.
33 Mutane sukan jefa kuri’a don su san nufin Allah, amma Allah da kansa ne yake ba da amsa.