1 Sa’ad da ka zauna cin abinci tare da babban mutum, ka tuna da yadda yake.
2 Idan kai mai son ci da yawa ne sai ka kanne.
3 Kada ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da yake gabanku, zai yiwu wayo yake so ya yi maka.
4 Ka zama mai isasshiyar hikima, kada ka gajiyar da kanka garin ƙoƙarin neman dukiya.
5 Kuɗinka sun iya ƙarewa kamar ƙyiftawar ido, kamar suna da fikafikai su tashi kamar gaggafa.
6 Kada ka ci abincin marowaci, ko ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da ya sa a gabanka.
7 Zai ce, “Bari a ƙara maka,” amma ba haka yake nufi ba. Kamar gashi yake a cikin maƙogwaronka.
8 Za ka harar da abin da ka ci, dukan daɗin bakinka zai tafi a banza.
9 Kada ka yi wa wawa magana irin ta haziƙai, gama ba zai yaba da maganarka ba.
10 Kada ka kuskura ka kawar da shaidar iyaka, ko ka ƙwace gonar marayu.
11 Ubangiji Mai Iko shi ne kāriyarsu, shi zai yi magana dominsu.
12 Ka mai da hankali ga malaminka, ka koyi dukan abin da kake iyawa.
13 Kada ka bar yaro ba horo, gama ko ka duke shi ba za a kashe shi ba.
14 Lalle ne za ka ceci ransa.
15 Ɗana, idan ka zama mai hikima zan yi murna ƙwarai.
16 Zan yi murna idan na ji kana faɗar magana da hikima.
17 Kada ka yi ƙyashin masu aikata zunubi tsoron Ubangiji kaɗai za ka sa a gaba.
18 Idan haka ta samu za ka yi farin ciki nan gaba.
19 Ka saurara, ya ɗana, ka zama mai hikima. Ka yi tunani mai zurfi a kan hanyarka.
20 Kada ka zauna da mashayan ruwan inabi, ko masu haɗama.
21 Gama bugaggu da ruwan inabi da masu zarin ci za su zama matalauta. Idan iyakar abin da kake yi daga ci sai barci ne, nan da nan za ka ga kana saye da tsummoki.
22 Ka kasa kunne ga mahaifinka, gama da ba dominsa ba, da ba ka, sa’ad da mahaifiyarka ta tsufa ka nuna mata godiyarka.
23 Gaskiya, da hikima, da ilimi, da hankali, sun cancanta a saye su, kome tamaninsu.
24 Mahaifin adali yana da dalilin yin murna. Zai yi fāriya a kan ɗa mai hikima.
25 Ka sa mahaifinka da mahaifiyarka su yi fāriya da kai, ka sa mahaifiyarka farin ciki.
26 Ɗana ka mai da hankali sosai, irin zamana ya zamar maka kyakkyawan misali.
27 Karuwa, da mata mazinata, tarkon mutuwa ne su.
28 Sukan laɓe su jira ka kamar mafasa, suna sa mutane da yawa su zama marasa aminci.
29 Wa ake yi wa kaito? Wa yake da baƙin ciki? Wane ne mafaɗaci? Wa yake yin gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan ido?
30 Sai riƙaƙƙen mashayi wanda yake gaurayar ruwan inabi.
31 Kada ka bar ruwan inabi ya jarabce ka, ko da yake ja wur yake, har kana iya ganin kanka a cikin ƙoƙon, yana kuwa da kyan gani sa’ad da kake motsa shi.
32 Kashegari za ka ji kamar maciji mai dafi ne ya sare ka.
33 Idanunka za su riƙa gane-gane, ba za ka iya tunani ko ka faɗi magana sosai ba.
34 Za ka ji kamar kana can cikin teku, jirin teku na ɗibarka kana lilo a kan rufin jirgin ruwa da yake tangaɗi.
35 Za ka ce, “Lalle an doke ni, sosai an daddoke ni amma ban san lokacin ba, me ya sa ban farka ba? Ina bukatar in ƙara sha.”