Gargaɗin Yin Biyayya
1 Ɗana kada ka manta da abin da na koya maka. Kullum ka tuna da abin da na faɗa maka ka yi.
2 Koyarwata za ta ba ka tsawon rai da wadata.
3 Kada ka yarda ka rabu da biyayya da aminci, ka ɗaura su a wuyanka, ka rubuta su kuma a zuciyarka.
4 Idan ka yi wannan kuwa, Allah zai yi murna da kai. Za ka yi nasara cikin hulɗar da kake yi da mutane.
5 Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani.
6 A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.
7 Sam, kada ka yarda ka ɗauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata mugunta.
8 Idan ka kiyaye wannan, zai zama maka kamar magani mai kyau, ya warkar da raunukanka, ya kuma sawwaƙe maka azabar da kake sha.
9 Ka girmama Ubangiji ta wurin miƙa masa hadaya daga mafi kyau na amfanin gonarka.
10 Idan ka yi haka rumbunanka za su cika da hatsi. Za ka sami ruwan inabi mai yawa, har ka rasa wurin da za ka zuba shi duka.
11 Ɗana, sa’ad da Ubangiji ya tsauta maka ka mai da hankali sosai, ka kuma yarda da gargaɗinsa.
12 Ubangiji yana tsauta wa waɗanda yake ƙauna. Kamar yadda mahaifi yakan tsauta wa ɗan da yake fāriya da shi.
13 Mai farin ciki ne mutumin da ya zama mai hikima, ya kuma sami fahimi.
14 Yana da riba mai yawan gaske fiye da ta azurfa, tamaninta a gare ka ya fi na zinariya.
15 Tamanin hikima ya fi na lu’ulu’ai, ya kuma fi kowane irin abin da kake so tamani.
16 Hikima takan tsawanta ranka, ta kuma ba ka dukiya da daraja.
17 Hikima takan sa ka ji daɗin zama, ta kuma bi da kai lafiya a zamanka.
18 Masu farin ciki ne waɗanda suka sami hikima, hikima za ta ba su rai kamar yadda itace yakan ba da ‘ya’ya.
19 Ubangiji ya halicci duniya ta wurin hikimarsa,
Ya shimfiɗa sararin sama a inda yake ta wurin saninsa.
20 Hikimarsa ta sa ruwan koguna ya yi gudu,
Gizagizai kuwa su zubo da ruwa bisa duniya.
21 Ɗana ka riƙe hikimarka da basirarka. Ko kusa kada ka bari su rabu da kai.
22 Za su tanada maka rai, rai mai daɗi da farin ciki.
23 Za ka bi hanyarka lafiya lau, ba ko tuntuɓe.
24 Ba za ka ji tsoro, sa’ad da kake kwance a gadonka ba, za ka yi ta sharar barci a dukan dare.
25 Ba za ka damu da masifar da za ta auko farat ɗaya ba, irin wadda takan auka wa mugaye kamar hadiri.
26 Ubangiji zai kiyaye ka. Ba zai bari ka fāɗa cikin tarko ba.
27 Ka yi wa masu bukata alheri a duk lokacin da kake iyawa.
28 Sam, kada ka ce wa maƙwabcinka ya dakata sai gobe, idan dai kana iya taimakonsa yanzu.
29 Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, gama yana zaune kusa da kai, yana kuwa amincewa da kai.
30 Kada ka yi jayayya ba dalili da wanda bai taɓa cutarka ba.
31 Kada ka ji kishin masu ta da zaune tsaye, ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu,
32 gama Ubangiji yana ƙin mutanen da suke aikata mugunta, amma yakan rungumi adalai ya amince da su.
33 Ubangiji yakan la’antar da gidajen masu mugunta, amma yakan sa wa gidajen adalai albarka.
34 Ba ruwansa da masu girmankai, amma masu tawali’u sukan sami tagomashi a wurinsa.
35 Mutane masu hikima za su sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.