Hikimar Agur
1 Waɗannan su ne maganar Agur ɗan Yake, da ya yi wa Etiyel da Yukal,
2 “Hakika wautata ta sa na zama kamar dabba ba mutum ba,
Ba ni kuwa da fahimi irin na mutum.
3 Ban koyi hikima ba,
Ban kuwa san kome game da Allah ba.
4 Wa ya taɓa hawa cikin Sama ya sauko?
Wa ya taɓa kama iska cikin tafin hannunsa?
Wa ya taɓa ƙunshe ruwa cikin rigarsa?
Wa kuma ya kafa iyakar duniya?
Ina sunansa, ina kuma sunan ɗansa?
Hakika ka sani!
5 “Kowace maganar Allah takan tabbata. Shi garkuwa ne ga waɗanda suke fakewa a wurinsa.
6 Kada ka yi ƙari a kan maganarsa, don kada ya tsauta maka, a kuma bayyana kai maƙaryaci ne.”
Waɗansu Karin Magana kuma
7 Abu biyu na roƙe ka, kada ka hana mini su kafin in mutu.
8 Ka kawar da ƙarya nesa da ni. Kada ka ba ni talauci ko dukiya, sai dai ka ba ni abinci daidai da bukatata,
9 don kada in wadata, har in yi musunka, in ce, “Wane ne Ubangiji?” Kada kuwa in yi talauci har in yi sata in saɓi sunan Allahna.
10 Kada ka kushe bara a wurin maigidansa domin kada ka yi laifin da zai sa a la’ance ka.
11 Akwai waɗansu mutane da sukan zagi iyayensu maza, ba sukan kuma nuna godiya ga iyayensu mata ba.
12 Akwai waɗansu mutanen da suke ganin kansu tsarkaka ne, alhali kuwa ƙazamai ne su.
13 Akwai waɗansu mutane da suke yi wa jama’a ƙallon raini suna ɗaurin gira.
14 Akwai waɗansu mutane waɗanda haƙoransu takuba ne, mataunansu kuma wuƙaƙe ne, don su cinye matalauta da masu fatara daga duniya.
15-16 Matsattsaku tana da ‘ya’ya mata biyu, ana kiransu, “Ba ni, Ba ni.”
Akwai abu uku da ba su ƙoshi, i, har huɗu ma da ba su cewa, “Ya isa,” wato
lahira,
macen da ba ta haihuwa,
ƙasa wadda ba ta ƙoshi da ruwa,
wuta wadda ba ta cewa, “Ya isa.”
17 Idan ɗa ya raina mahaifi, ya kuma yi wa mahaifiya ba’a hankakin kwari za su ƙwaƙule masa idanu, ‘ya’yan mikiya za su cinye.
18-19 Akwai abu uku, i, har huɗu ma, waɗanda ban iya fahimtar su ba, wato
yadda gaggafa take tashi a sararin sama,
yadda maciji yake jan ciki a kan dutse,
yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku,
Sha’anin namiji da ‘ya mace.
20 Ga yadda al’amarin mazinaciya yake, takan yi sha’aninta sa’an nan ta yi wanka ta ce, “Ban yi laifin kome ba!”
21-23 Akwai abu uku, i, har huɗu ma waɗanda duniya ba ta jurewa da su, wato
bara da ya zama sarki,
wawa da ya ƙoshi da abinci,
mummunar mace da ta sami miji,
baiwar da ta gāji uwargijiyarta.
24-28 Akwai ƙananan abubuwa huɗu a duniya, amma suna da hikima ƙwarai, wato
tururuwa talikai ne marasa ƙarfi, amma duk da haka sukan tanadi abincinsu da rani,
remaye ba ƙarfafa ba ne, duk da haka suna yi wa kansu gidaje a cikin duwatsu,
fara ba su da sarki, amma duk da haka suna tafiya sahu-sahu.
ƙadangare ma wanda ka iya kama shi a hannu, amma yana zama a cikin fādodin sarakuna.
29-31 Akwai abu uku, i, har huɗu ma da suke da kwarjini da taƙama a tafiyarsu, wato
Zaki wanda ya fi dukan dabbobi ƙarfi, ba ya ratse wa kowa daga cikinsu,
bunsuru da zakara mai taƙama,
sarkin da yake tafiya gaban jama’arsa.
32 Idan ka yi wauta kana ta ɗaukaka kanka, ko kuwa kana shirya mugunta, ka tsaya ka yi tunani!
33 Gama kaɗa madara takan kawo mai, murɗa hanci takan sa a yi haɓo, tsokanar fushi takan kawo jayayya.