Faɗakarwa a kan Fasikanci
1 Ɗana, ka mai da hankali, ka kasa kunne ga hikimata da basirata.
2 Sa’an nan ne za ka san yadda za ka yi kome daidai, kalmominka za su nuna kana da ilimi.
3 Leɓunan matar wani, mai yiwuwa ne, su yi zaƙi kamar zuma, sumbace-sumbacenta kuma su fi man zaitun taushi.
4 Amma bayan an gama duka, ba abin da za ta bar maka sai baƙin ciki, da azaba.
5 Za ta gangara da kai zuwa lahira, hanyar da take bi hanyar mutuwa ce.
6 Ba a kan hanyar rai take ba, tana ragaita nesa da hanyar, amma kai ba ka ankara ba.
7 ‘Ya’yana, ku kasa kunne gare ni yanzu, kada ko kusa ku manta da abin da nake faɗa.
8 Ku yi nesa da irin wannan mace! Kada ku yarda ku yi ko kusa da ƙofarta!
9 Idan kuwa kun yi, girmamawar da ake yi muku za ta zama ta waɗansu. Za ku yi mutuwar ƙuruciya ta hannun mutane marasa imani.
10 Hakika, baƙi za su kwashe dukan dukiyarku, abin da kuka sha wahalar samu kuma zai zama rabon wani dabam.
11 Za ku kwanta kuna nishi a kan gadon mutuwa, namanku da tsokokinku za su zagwanye.
12 Sa’an nan za ku ce, “Me ya sa ban taɓa koyo ba? Me ya sa ban yarda wani ya kwaɓe ni ba?
13 Ban kasa kunne ga malamaina ba. Ban mai da hankalina gare su ba.
14 Farat ɗaya sai aka kunyatar da ni a bainar jama’a.”
15 Ka yi aminci ga matarka, ka ƙaunace ta ita kaɗai.
16 Idan kuma waɗansu mata sun haifa maka ‘ya’ya, ‘ya’yan nan ba za su yi maka wani amfani ba.
17 ‘Ya’yanka za su yi girma su taimake ka, ba na baƙi ba.
18 Saboda haka ka yi farin ciki tare da matarka, ka yi murna da budurwa da ka auro,
19 kyakkyawa mai kyan gani kamar barewa. Bari kyanta ya ɗau hankalinka. Bari ƙaunarta ta kewaye ka.
20 Ɗana, don me za ka fi son matar wani? Don me za ka bar matar wani ta lallame ka da daɗin bakinta?
21 Ubangiji yana ganin dukan abin da kake yi. Inda ka shiga duk yana kallonka.
22 Zunuban mutum tarko ne, komar zunubinsa ce take kama shi.
23 Yakan mutu saboda rashin kamewarsa, cikakkiyar wautarsa za ta kai shi kabarinsa.