Wayon Mazinaciya
1 Ɗana, ka tuna da abin da na faɗa, kada ka manta da abin da na ce maka ka yi.
2 Ka yi abin da na faɗa maka, za ka rayu. Ka natsu, ka bi koyarwata, ka tsare ta kamar ƙwayar idonka.
3 Kullayaumi ka riƙe koyarwata tare da kai, ka rubuta ta a zuciyarka.
4 Ka mai da hikima ‘yar’uwarka, basira kuwa ta zama ƙawarka ta jikinka.
5 Za su nisanta ka da matan mutane, daga kuma mata masu maganganun alfasha.
6 Wata rana ina leƙawa ta tagar ɗakina,
7 sai na ga waɗansu samari masu yawa waɗanda ba su gogu da duniya ba, musamman sai na lura da wani dolo a cikinsu.
8 Yana tafe a kan titi kusa da kusurwar da take a zaune, yana wucewa kusa da gidanta,
9 da magariba cikin duhu.
10 Sai ta tarye shi, ta ci ado kamar karuwa, tana shirya yadda za ta yaudare shi.
11 (Ba ta jin tsoro, ba ta kuma jin kunya, ko yaushe tana ta gantali a tituna.
12 Takan tsaya tana jira a kowace kusurwa, wani lokaci a tituna, wani lokaci kuma a kasuwa.)
13 Ta rungumi saurayin, ta sumbace shi, ta dubi tsabar idonsa ta ce,
14 “Na miƙa hadayu yau, ina da nama na hadayu.
15 Shi ya sa na fito ina nemanka, ina so in gan ka, ga shi kuwa, na gan ka!
16 Na lulluɓe gadona da zannuwan lilin masu launi iri iri daga Masar.
17 Na yayyafa musu turaren mur da na aloyes da na kirfa.
18 Ka zo mu sha daɗin ƙauna, mu more dukan dare, mu yi farin ciki rungume da juna.
19 Mijina ba ya gida, ya yi tafiya mai nisa.
20 Ya tafi da kuɗi masu yawa, ba zai komo ba sai bayan mako biyu.”
21 Ta jarabce shi da kwarkwasarta, sai ya ba da kai ga daɗin bakinta.
22 Nan da nan ya bi ta kamar sā zuwa mayanka, kamar barewa tana tsalle zuwa cikin tarko,
23 inda kibiya za ta soke zuciyarta. Yana kama da tsuntsun da yake zuwa cikin tarko, bai kuwa sani ransa yana cikin hatsari ba.
24 Yanzu fa ‘ya’yana, ku kasa kunne gare ni, ku mai da hankali ga abin da nake faɗa.
25 Kada ku yarda irin wannan mace ta rinjayi zuciyarku, kada ku yi ta yawon nemanta.
26 Ita ce sanadin hallakar mutane da yawa, ta sa mutane da yawa mutuwa, har ba su ƙidayuwa.
27 Tafiya gidanta kuna kan hanya zuwa mutuwa ke nan, gajeruwar hanya ce zuwa lahira.