Waɗansu Mata sun Tafi tare da Yesu
1 Ba da daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa’azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi,
2 da waɗansu mata da aka raba da baƙaƙen aljannu da kuma rashin lafiyarsu. Cikinsu da Maryamu mai suna Magadaliya, wadda aka fitar wa da aljannu bakwai,
3 da Yuwana matar Kuza, wakilin Hirudus, da Suzanatu, da kuma waɗansu da yawa da suka yi musu ɗawainiya da kayansu.
Misali na Mai Shuka
4 Da jama’a masu yawa suka taru, mutane suna ta zuwa gare shi gari da gari, sai ya yi musu misali ya ce.
5 “Wani mai shuka ya tafi shuka. Yana cikin yafa iri sai waɗansu suka fāɗi a hanya, aka tattake su, tsuntsaye suka tsince su.
6 Waɗansu kuma suka fāɗi a dutse. Da suka tsiro sai suka bushe, don ba danshi.
7 Waɗansu kuma suka fāɗi cikin ƙaya, suka tashi tare, har ƙayar ta sarƙe su.
8 Waɗansu kuwa suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka girma, suka yi ƙwaya riɓi ɗari ɗari.” Da ya faɗi haka, sai ya ta da murya ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”
Manufar Misalin
9 Almajiransa suka tambaye shi ma’anar misalin.
10 Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.
Yesu Ya Ba da Bayanin Misalin Mai Shuka
11 “To, misalin shi ne, irin Maganar Allah ne.
12 Waɗanda suka fāɗi a hanya su ne kwatancin waɗanda suka ji Maganar Allah, sa’an nan Iblis ya zo ya ɗauke Maganar daga zuciyarsu, don kada su ba da gaskiya su sami ceto.
13 Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya ‘yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe.
14 Waɗanda suka fāɗi cikin ƙaya kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, amma a kwana a tashi, sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya su sarƙe su, har su kasa yin amfani.
15 Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, suka riƙe ta kamkam da zuciya ɗaya kyakkyawa, suka jure har suka yi amfani.
Fitila a Rufe da Masaki
16 “Ba mai kunna fitila ya rufe ta da masaki, ko ya ajiye ta a ƙarƙashin gado. A’a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken.
17 Ba abin da yake a ɓoye da ba za a bayyana ba. Ba kuma asirin da ba zai tonu ya zama bayyananne ba.
18 Ku kula fa, ku iya ji, don mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake tsammani yake da shi ma, sai a karɓe masa.”
Uwar Yesu da ‘Yan’uwansa
19 Uwa tasa da ‘yan’uwansa suka zo wurinsa, amma suka kasa isa gunsa saboda taro.
20 Sai aka ce masa, “Tsohuwarka da ‘yan’uwanka suna tsaye a waje, suna son ganinka.”
21 Amma ya amsa musu ya ce, “Masu jin Maganar Allah, suna kuma aikata ta, ai, su ne uwata, su ne kuma ‘yan’uwana.”
Yesu Ya Tsawata wa Hadiri
22 Wata rana ya shiga jirgi tare da almajiransa. Ya ce musu, “Mu haye wancan hayin teku.” Sai suka tashi.
23 Suna cikin tafiya sai barci ya kwashe shi. Hadiri mai iska ya taso a tekun, jirginsu ya tasar wa cika da ruwa, har suna cikin hatsari.
24 Suka je suka tashe shi, suka ce, “Maigida, Maigida, mun hallaka!” Ya farka, ya tsawata wa iskar da kuma haukan ruwa. Sai suka kwanta, wurin ya yi tsit.
25 Ya ce musu, “Ina bangaskiyarku?” Suka kuwa tsorata suka yi mamaki, suna ce wa juna, “Wa ke nan kuma, har iska da ruwa ma yake yi wa umarni, suna kuwa yi masa biyayya?”
Warkar da Mai Aljan na Garasinawa
26 Sai suka iso ƙasar Garasinawa wadda take hannun riga da ƙasar Galili.
27 Da saukarsa a gaci sai wani mai aljannu ya fito daga cikin gari ya tarye shi. Ya daɗe bai sa tufa ba, ba ya zama a gida kuwa, sai a makabarta.
28 Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya faɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, ya Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.”
29 Ya faɗi haka ne domin Yesu ya umarci baƙin aljanin ya rabu da mutumin. Gama sau da yawa aljanin yakan buge shi, akan kuma tsare shi, a ɗaure shi da sarƙa da mari, amma ya tsintsinka ɗaurin, aljanin ya kora shi jeji.
30 Sai Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Tuli,” don aljannu da yawa sun shiga cikinsa.
31 Sai suka yi ta roƙansa kada ya umarce su su fāɗa a mahalaka.
32 To, wurin nan kuwa akwai wani babban garkin alade na kiwo a gangaren dutse, suka roƙe shi ya yardar musu su shiga cikinsu. Ya kuwa yardar musu.
33 Sai aljannun suka rabu da mutumin, suka shiga aladun. Garken kuwa suka rungungunta ta gangaren, suka faɗa tekun, suka halaka a ruwa.
34 Da ‘yan kiwon aladen nan suka ga abin da ya faru, suka gudu, suka ba da labari a birni da ƙauye.
35 Sai jama’a suka firfito su ga abin da ya auku. Suka zo wurin Yesu, suka tarar da mutumin da aljannun suka rabu da shi, zaune gaban Yesu, saye da tufa, yana cikin hankalinsa. Sai suka tsorata.
36 Waɗanda aka yi abin a idonsu kuwa, suka gaya musu yadda aka warkar da mai aljannun nan.
37 Dukan mutanen kewayen ƙasar Garasinawa suka roƙi Yesu ya rabu da su, don tsoro mai yawa ya kama su. Sai ya shiga jirgi ya koma.
38 Mutumin da aljannun suka rabu da shi kuwa, ya roƙe shi izinin tafiya tare da shi. Amma ya sallame shi ya ce,
39 “Koma gida, ka faɗi irin manyan abubuwan da Allah ya yi maka.” Sai ya tafi ko’ina a cikin birnin yana sanar da manyan abubuwan da Yesu ya yi masa.
Warkar da ‘Yar Yayirus da Matar da ta Taɓa Gezar Mayafin Yesu
40 To, da Yesu ya komo, taron suka yi masa maraba domin ko a dā ma duk suna jiransa ne.
41 Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, wani shugaban majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya roƙe shi ya je gidansa.
42 Yana da ‘ya ɗaya tilo, mai shekara misalin goma sha biyu, tana kuma bakin mutuwa.
Yana tafiya, taro masu yawa na matsa tasa,
43 sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta kuma ɓad da duk abin hannunta wajen masu magani, ba wanda ya iya warkar da ita.
44 Ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa. Nan take zubar jininta ta tsaya.
45 Sai Yesu ya ce, “Wa ya taɓa ni?” Da kowa ya yi mūsū, Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka ce, “Maigida, ai, taro masu yawa ne suke tutturarka, suna matsarka.”
46 Amma Yesu ya ce, “An dai taɓa ni, domin na ji iko ya fita daga gare ni.”
47 Da matar ta ga ba dama ta ɓuya, sai ta matso tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta bayyana a gaban duk jama’a dalilin da ya sa ta taɓa shi, da kuma yadda ta warke nan take.
48 Sai ya ce mata, “’Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”
49 Yana cikin magana, sai ga wani ya zo daga gidan shugaban majami’ar, ya ce, “Ai, ‘yarka ta rasu. Kada ka ƙara wahalar da Malamin.”
50 Amma da Yesu ya ji haka, ya amsa ya ce wa shugaban majami’ar, “Kada ka ji tsoro. Ka ba da gaskiya kawai, za ta kuwa warke.”
51 Da ya isa gidan bai yarda kowa ya shiga tare da shi ba, sai Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da kuma uban yarinyar da uwa tata,
52 Duk kuwa ana ta kuka da kururuwa saboda ita. Amma Yesu ya ce, “Ku daina kuka. Ai, ba matacciya take ba, barci take yi.”
53 Sai suka yi masa dariyar raini, don sun sani ta mutu.
54 Shi kuwa sai ya riƙe hannunta, ya ta da murya ya ce, “Yarinya, ki tashi.”
55 Ruhunta kuwa ya dawo, nan take ta tashi. Sai ya yi umarni a ba ta abinci.
56 Iyayenta suka yi mamaki. Amma ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da ya faru.