Kome Banza Ne
1 Maganar Mai Wa’azi ɗan Dawuda, Sarkin Urushalima.
2 Banza a banza ne, in ji Mai Hadishi,
Banza a banza ne, dukan kome banza ne.
3 Wace riba ce mutum zai samu daga cikin aikinsa,
Da yake yi a duniya?
4 Zamani yakan wuce, wani zamani kuma ya zo,
Amma abadan duniya tana nan yadda take.
5 Rana takan fito, takan kuma faɗi,
Sa’an nan ta gaggauta zuwa wurin fitowarta.
6 Iska takan hura zuwa kudu, ta kuma hura zuwa arewa,
Ta yi ta kewayawa, har ta koma inda ta fito.
7 Kowane kogi yakan gangara zuwa teku,
Amma har yanzu teku ba ta cika ba.
Ruwan yakan koma mafarin kogin,
Ya sāke gangarawa kuma.
8 Kowane abu yana sa gajiya,
Gajiyar kuwa ta fi gaban magana.
Idanunmu ba sā ƙoshi da gani,
Haka kuma kunnuwanmu ba sā ƙoshi da ji.
9 Abin da ya faru a dā, shi zai sāke faruwa,
Abin da aka yi a dā, shi za a sāke yi.
A duniya duka ba wani abu da yake sabo.
10 Da akwai wani abu da za a ce,
“Duba, wannan sabon abu ne”?
Abin yana nan tuntuni kafin zamaninmu.
11 Ba wanda yake iya tunawa da abin da ya faru a dā,
Da abin da zai faru nan gaba.
Ba wanda zai iya tunawa da abin da zai faru
A tsakanin wannan lokaci da wancan.
Abin da Mai Hadishi Ya Kware da Shi
12 Ni Mai Hadishi sarki ne, na sarauci Isra’ilawa a Urushalima.
13 Na ɗauri aniya in jarraba, in bincika dukan abubuwan da ake yi a duniyan nan.
Allah ya ƙaddara mana abu mai wuya.
14 Na ga dukan abin da ake yi a duniya, duk aikin banza ne da ɓata lokaci kawai.
15 Ba za a iya miƙar da abin da ya tanƙware ba, ba kuma za a iya ƙidaya abin da ba shi ba.
16 Na ce wa kaina, “Na zama babban mutum, na fi duk wanda ya taɓa mulkin Urushalima hikima. Hakika na san hikima da ilimi.”
17 Na ɗaura aniya in san bambancin da yake tsakanin ilimi da wauta, da a tsakanin hikima da gāɓanci. Amma na gane harbin iska nake yi kawai.
18 Gwargwadon hikimarka gwargwadon damuwarka, gwargwadon ƙarin iliminka gwargwadon jin haushinka.