1 Na sa rai in ji wa kaina daɗi, in kuma san yadda farin ciki yake. Sai na tarar wannan ma aikin banza ne.
2 Na kuma gane dariya wauta ce, nishaɗi kuma ba shi da wani amfani.
3 Muradina shi ne in san hikima in nemi yadda zan ji wa raina daɗi da ruwan inabi, in sa kaina ga aikata wawanci. Bisa ga tsammanina mai yiwuwa ne wannan shi ne abu mafi kyau da mutane za su yi a duniya, a ‘yan kwanakinsu.
4 Na kammala manyan abubuwa. Na gina wa kaina gidaje, na yi gonakin inabi.
5 Na kuma yi wa kaina lambuna da gonakin itatuwa, ba irin itatuwa masu ‘ya’ya da ba su a ciki.
6 Na yi tafkuna na yi wa itatuwana banruwa.
7 Na sayo bayi mata da maza, an kuma haifa mini cucanawa a gidana. Ina kuma da manyan garkunan shanu, da na tumaki, da na awaki fiye da dukan wanda ya taɓa zama a Urushalima.
8 Na tara wa kaina azurfa, da zinariya, daga baitulmalin ƙasashen da nake mulki. Mawaƙa mata da maza suna raira mini waƙa, ina da dukan irin matan da kowane namiji zai so.
9 I, na ƙasaita fiye da dukan waɗanda suka riga ni zama a Urushalima. Hikimata kuma ba ta taɓa rabuwa da ni ba.
10 Duk abin da nake so, na samu, ban taɓa hana wa kaina kowane irin nishaɗin da nake so ba. Ina fariya da kowane irin abin da na aikata. Wannan shi ne ladana na dukan aikina.
11 Na yi tunani a kan dukan abin da na aikata, da irin wahalar da na sha lokacin da nake yin aikin, sai na gane ba shi da wata ma’ana, na zama kamar mai harbin iska, ba shi da wani amfani.
12 Bayan wannan duka, abin da sarki zai iya yi kaɗai, shi ne abin da sarakunan da suka riga shi suka yi.
Sai na fara tunani a kan abin da ake nufi da hikima, ko rashin kula, ko wauta.
13 To, na sani hikima ta fi wauta, kamar yadda haske ya fi duhu.
14 Mai hikima ya san inda ya nufa, amma wawa ba zai iya sani ba. Na kuma sani makomarsu guda ce.
15 A zuciyata na ce, “Abin da yakan sami wawa shi ne kuma zai same ni. To, wace riba na ci ke nan saboda hikimar da nake da ita?” Na kuma ce a zuciyata, “Wannan ma aikin banza ne.”
16 Gama ba za a ƙara tunawa da mai hikima ko wawa ba, nan gaba za a manta da dukansu. Yadda mai hikima yake mutuwa haka ma wawa yake mutuwa.
17 Saboda haka rai ba wani abu ba ne a gare ni, domin dukan abin da yake cikinsa bai kawo mini kome ba sai wahala. Duka banza ne, ba abin da nake yi sai harbin iska kawai.
18 Daga cikin dukan abin da na samu kan aikin da na yi, ba su da wata ma’ana a gare ni, gama na sani zan bar wa magājina ne.
19 Wa ya sani ko shi mai hikima ne, ko kuma wawa ne? Duk da haka shi zai mallaki dukan abin da na sha wahalar tanadinsa. Dukan aikin da na yi na hikima a wannan duniya aikin banza ne.
20 Na yi baƙin ciki a kan dukan wahalar aikin da na yi a duniya.
21 Kai ne ka yi aiki da dukan hikimarka, da iliminka, da gwanintarka, amma kuma tilas ka bar shi duka ga wanda bai yi wahalar kome a ciki ba. Wannan ma bai amfana kome ba, mugun abu ne.
22 Me mutum zai samu daga cikin aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin?
23 Dukan abin da yake yi a kwanakinsa, ba abin da ya jawo masa, sai damuwa da ɓacin zuciya. Da dare ma ba ya iya hutawa. Wannan kuma aikin banza ne duka.
24 Ba abin da ya fi wa mutum kyau fiye da ya ci, ya sha, ya saki jiki, ya ci moriyar aikinsa. Na gane wannan ma daga wurin Allah ne.
25 Ƙaƙa za ka sami abin da za ka ci, ko ka ji daɗin zamanka in ba tare da shi ba?
26 Allah ne yake ba da hikima, da ilimi, da farin ciki ga wanda yake ƙauna. Amma yakan sa matalauci, mai zunubi, ya yi ta wahalar nema ya tara dukiya, domin Allah ya bayar ga wanda yake ƙauna. Wannan ma aikin banza ne, harbin iska ne kawai.