Fifikon Hikima
1 Kyakkyawan suna ya fi man ƙanshi tsada, ranar mutuwa kuma ta fi ranar haihuwa.
2 Gara a tafi gidan da ake makoki
Da a tafi gidan da ake biki,
Gama wannan shi ne ƙarshen dukan mutane.
Ya kamata duk mai rai ya riƙe wannan a zuciyarsa,
Mutuwa tana jiran kowa.
3 Baƙin ciki ya fi dariya,
Gama baƙin ciki yakan kawo gyara.
4 Mai hikima yakan yi tunanin mutuwa,
Amma wawa yakan yi tunanin shagalin duniya.
5 Gara mutum ya ji tsautawar mai hikima,
Da ya ji wawaye suna yabonsa.
6 Dariyar wawa kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya ce.
Wannan ma aikin banza ne.
7 Hakika zalunci yakan sa mai hikima ya zama wawa,
Karɓar rashawa kuma yakan lalata hali.
8 Gara ƙarshen abu da farkonsa.
Mai haƙuri kuma ya fi mai girmankai.
9 Ka kame fushinka,
Gama wawa ne yake cike da fushi.
10 Kada ka yi tambaya, cewa me ya sa zamanan dā suka fi na yanzu?
Gama wannan tambaya ba ta hikima ba ce.
11 Ya kamata kowane mutum ya zama mai hikima,
Gama tana da kyau kamar cin gādo.
12 Hikima mafaka ce, takan kāre mutum kamar yadda kuɗi yake yi.
Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita, ita ce amfanin ilimi.
13 Ka yi tunanin aikin Allah,
Wa ya isa ya miƙe abin da ya tanƙware?
14 In kana jin daɗi, ka yi murna,
In kuma wahala kake sha, ka tuna,
Allah ne ya yi duka biyunsa,
Don kada mutum ya san abin da zai faru a nan gaba.
15 A kwanakina marasa amfani na ga kowane irin abu. Adali ba safai yakan yi tsawon rai ba, mugu kuwa yakan yi tsawon rai a mugayen ayyukansa.
16 Kada ka cika yin adalci, kada kuma ka cika yin hikima, gama don me za ka kashe kanka?
17 Kada ka cika yin mugunta, kada kuma ka cika yin wauta, gama don me za ka mutu tun kwanakinka ba su cika ba?
18 Idan ka riƙe wannan zai amfane ka. Kada ka bar wancan, gama shi wanda yake tsoron Allah zai yi amfani da su.
19 Abin da hikima take iya yi wa mutum ɗaya ya fi abin da masu mulki goma za su yi wa birni.
20 Ba wani mutum a duniyan nan wanda yake aikata abin da yake daidai dukan lokaci, ba tare da yin kuskure ba.
21 Kada ka kula da kowane abu da mutane suke faɗa, mai yiwuwa ne ka ji baranka yana zaginka.
22 Kai kanka ka sani sau da yawa kakan zagi waɗansu mutane.
Neman Hikima
23 Na yi amfani da hikimata don in jarraba wannan duka, domin na ɗaura aniya in zama mai hikima, amma abin ya fi ƙarfina.
24 Wane ne zai iya sanin gaibi? Abin ya yi mana zurfi ƙwarai, yana da wuyar ganewa.
25 Amma na duƙufa neman ilimi, ina ta yin nazari, ina nema in san hikima da amsoshin tambayoyina, in kuma san mugunta da wautar dakikanci.
26 Sai na iske wani abu da ya fi mutuwa ɗaci, wato mace wadda ƙaunar da take yi maka za ta kama ka kamar tarko, kamar kuma raga. Rungumewar da za ta yi maka za ta ɗaure ka kamar sarƙa. Wanda Allah yake jin daɗinsa zai tsere mata, amma za ta kama mai zunubi.
27 Haka ne, in ji Mai Hadishi, da kaɗan da kaɗan na gane wannan sa’ad da nake neman amsa.
28 Amsar da nake nema ban samu ba. Na sami mutum ɗaya mai hikima, wato a cikin mutum dubu, amma daga cikin mata ban sami ko ɗaya ba.
29 Wannan ne kaɗai abin da na gane, tsaf Allah ya yi mu, amma mu muka rikitar da kanmu.