MAK 3

Sa Zuciya ga Samun Taimako daga Wurin Ubangiji

1 Ni ne mutumin da ya sha wuyar horon Ubangiji.

2 Ya kore ni zuwa cikin duhu baƙi ƙirin.

3 Hakika ikonsa ya yi ta gāba da ni dukan yini.

4 Ya sa naman jikina da fatar jikina su lalace,

Ya kuma kakkarya ƙasusuwana.

5 Ya kewaye ni da yaƙi,

Ya rufe ni da baƙin ciki mai tsanani da wahala.

6 Ya zaunar da ni cikin duhu,

Kamar waɗanda suka daɗe da mutuwa.

7 Ya kewaye ni da garu don kada in tsere,

Ya ɗaure ni da sarƙa mai nauyi.

8 Ko da yake ina kira, ina kukan neman taimako,

Ya yi watsi da addu’ata.

9 Ya toshe hanyata da sassaƙaƙƙun duwatsu,

Ya karkatar da hanyoyina.

10 Ya zamar mini kamar beyar wanda yake fako,

Kamar zaki a ɓoye cikin ruƙuƙi.

11 Ya bauɗar da ni daga hanyata, ya yayyage ni,

Ya maishe ni, ba ni a kowa.

12 Ya ja bakansa, ya sa in zama abin baratarsa.

13 Ya harbe zuciyata da kiban kwarinsa.

14 Na zama abin dariya ga dukan mutane,

Dukan yini suna yi mini waƙar zambo.

15 Ya shayar da ni da ruwan ɗaci,

Ya ƙosar da ni da abinci mai ɗaci.

16 Ya sa in tauna tsakuwa da haƙorana,

Ya zaunar da ni cikin ƙura.

17 An raba ni da salama,

Na manta da abar da ake ce da ita wadata.

18 Sai na ce, “Darajata ta ƙare,

Ba ni kuma da sa zuciya wurin Ubangiji.”

19 Ka tuna da azabata, da galabaitata,

Da ɗacin raina, da kumallon da nake fama da shi.

20 Kullum raina yana tunanin azabaina,

Raina kuwa ya karai.

21 Da na tuna da wannan, sai na sa zuciya ga gaba.

22 Ƙaunar Ubangiji ba ta ƙarewa,

Haka kuma jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

23 Su sababbi ne kowace safiya,

Amincinka kuma mai girma ne.

24 Na ce, “Ubangiji shi ne nawa,

Saboda haka zan sa zuciya gare shi.”

25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke sauraronsa,

Da wanda suke nemansa kuma.

26 Yana da kyau a jira ceton Ubangiji da natsuwa,

27 Yana da kyau mutum ya hori kansa tun yana yaro.

28 Bari ya zauna a kaɗaice, ya yi shiru

Sa’ad da yake da damuwa.

29 Bari ya kwanta cikin ƙura,

Watakila akwai sauran sa zuciya.

30 Bari ya yarda a mari kumatunsa,

Ya haƙura da cin mutunci.

31 Gama Ubangiji ba zai yashe mu har abada ba.

32 Ko da ya sa ɓacin rai,

Zai ji tausayi kuma,

Saboda tabbatacciyar ƙaunarsa mai yawa.

33 Gama ba da gangan ba ne yakan wahalar da ‘yan adam

Ko ya sa su baƙin ciki.

34 Ubangiji bai yarda a danne

‘Yan kurkuku na duniya ba.

35 Bai kuma yarda a hana wa mutum hakkinsa

A gaban Maɗaukaki ba,

36 Ko kuwa a karkatar wa mutum da shari’arsa.

37 Wa ya umarta, abin kuwa ya faru,

In ba Ubangiji ne ya umarta ba?

38 Ba daga bakin Maɗaukaki

Alheri da mugunta suke fitowa ne ba?

39 Don me ɗan adam

Zai yi gunaguni a kan hukuncin zunubansa?

40 Bari mu jarraba, mu bincika hanyoyinmu,

Sa’an nan mu komo wurin Ubangiji.

41 Bari mu roƙi Allah na Sama,

Muna miƙa hannuwanmu sama, mu ce,

42 “Mun yi zunubi, mun tayar,

Kai kuwa ba ka gafarta ba.

43 “Ka yafa fushi, ka runtume mu,

Kana karkashe mu ba tausayi.

44 Ka kuma rufe kanka da gajimare

Don kada addu’a ta kai wurinka.

45 Ka maishe mu shara da juji a cikin mutane.

46 “Dukan maƙiyanmu suna yi mana ba’a.

47 Tsoro, da wushefe,

Da lalatarwa, da hallakarwa sun auka mana.

48 Hawaye suna gangarawa daga idanuna kamar ruwan koguna,

Saboda an hallaka mutanena.

49 “Hawayena suna ta gangarawa, ba tsayawa, ba hutawa,

50 Har lokacin da Ubangiji daga Sama ya duba, ya gani.

51 Ganin azabar ‘yan matan birnina

Ya sa ni baƙin ciki.

52 “Waɗanda suke maƙiyana ba dalili

Sun farauce ni kamar tsuntsu.

53 Sun jefa ni da rai a cikin rami,

Suka rufe ni da duwatsu.

54 Ruwa ya sha kaina,

Sai na ce, ‘Na halaka.’

55 “Ya Ubangiji, na yi kira ga sunanka

Daga cikin rami mai zurfi.

56 Ka kuwa ji muryata.

Kada ka rufe kunnenka ga jin kukana na neman taimako.

57 Sa’ad da na yi kira gare ka, ka zo kusa.

Sa’an nan ka ce mini kada in ji tsoro.

58 “Ka karɓi da’awata, ya Ubangiji,

Ka kuwa fanshi raina.

59 Ka ga laifin da aka yi mini,

Sai ka shara’anta da’awata, ya Ubangiji.

60 Ka ga dukan irin sakayyarsu,

Da dukan dabarun da suke yi mini.

61 “Ya Ubangiji, ka ji zargi

Da dukan dabarun da suke yi mini.

62 Leɓunan maƙiyana da tunaninsu

Suna gāba da ni dukan yini.

63 Suna raira mini waƙar zambo sa’ad da suke zaune,

Da lokacin da suka tashi.

64 “Ya Ubangiji, za ka sāka musu bisa ga ayyukansu,

65 Za ka ba su tattaurar zuciya,

La’anarka kuwa za ta zauna a kansu!

66 Da fushi za ka runtume su

Har ka hallaka su a duniya, ya Ubangiji!”