1 “Yanzu firistoci, ga umarni dominku.
2 Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la’ana, zan la’antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la’antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
3 Ga shi, zan tsauta wa ‘ya ‘yanku, in watsa kāshin dabbobin hadayunku a fuskokinku, sa’an nan zan kore ku daga gabana.
4 Ta haka za ku sani ni na ba ku wannan umarni domin alkawarin da na yi wa Lawi ya tabbata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
5 “Alkawarin da na yi masa na rai ne da salama. Na yi masa alkawaran kuma domin ya ji tsorona, yana kuwa tsorona. Yana kuma tsoron sunana ƙwarai.
6 Koyarwar gaskiya tana cikin bakinsa, ba a sami kuskure a bakinsa ba. Ya yi tafiya tare da ni da salama da gaskiya. Ya kuwa juyo da mutane da yawa daga mugunta.
7 Gama ya kamata bakin firist ya kiyaye ilimi, wajibi ne firistoci su koyar da ilimin gaskiya na Allah, a gare su mutane za su tafi su koyi nufina, domin su manzannina ne, ni Ubangiji Mai Runduna.
8 “Amma ku firistoci kun kauce daga hanya. Kun sa mutane da yawa su karkace saboda koyarwarku. Kun keta alkawarin da na yi da ku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
9 Saboda haka, ni ma zan sa jama’ar Isra’ila su raina ku, su ƙasƙantar da ku a gaban dukan mutane, domin ba ku kiyaye umarnina ba, sa’ad da kuke koyar da nufina, kun yi tara.”
Rashin Amincin Isra’ilawa
10 Ashe, ba dukanmu Ubanmu ɗaya ba ne? Ba Allah nan ɗaya ya halicce mu ba? To, me ya sa muke keta alkawarin da muka yi wa junanmu, muna raina alkawarin da Allah ya yi wa kakanninmu?
11 Mutanen Yahuza sun keta alkawarin da yake tsakaninsu da Allah, sun aikata mugun abu a Isra’ila, da a Urushalima. Gama sun ƙazantar da Haikalin da Ubangiji yake ƙauna, sun kuma auro matan da suke bauta wa gumaka.
12 Ubangiji zai lalatar da dukan wanda ya aikata wannan, wato wanda ya farka da wanda ya amsa, ko wanda yake kawo hadayu ga Ubangiji Mai Runduna.
13 Ga kuma abin da kuke yi. Kuna cika bagaden Ubangiji da hawaye, da kuka, da kururuwa domin ba zai ƙara karɓar hadayun da kuke kawo masa ba.
14 Kuna tambaya cewa, “Me ya sa ba ya karɓar hadayunmu?” Ai, domin ya sani ka keta alkawarin da ka yi wa matarka ta ƙuruciya ne, wadda ka ci amanarta ko da yake ita abokiyar zamanka ce, da matarka.
15 Ashe, ba kai da ita Allah ya maishe ku jiki ɗaya da ruhu ɗaya ba? Me Allah yake nufi da wannan? Yana so ‘ya’yanmu su zama ‘yan halal masu tsoron Allah. Domin haka ku kula fa, kada kowa ya ci amanar matarsa ta ƙuruciya.
16 “Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, na ce ina ƙin kisan aure, ina ƙinsa sa’ad da waninku ya yi wa matarsa haka nan. Domin haka sai ku kula da kanku kada ku keta alkawari, mutum ya zama mai aminci ga matarsa.”
Ranar Hukunci Ta Gabato
17 Kun gajiyar da Ubangiji Mai Runduna da maganganunku, amma kun ce, “Ƙaƙa muka gajiyar da shi?” Kuna cewa, “Ubangiji yana ganinsu, dukan masu aikata mugunta mutanen kirki ne, yana kuwa ƙaunarsu.” Kuna kuma cewa, “Ina Allah yake wanda yake shi adali ne?”