MAR 1

Wa’azin Yahaya Maibaftisma

1 Farkon bisharar Yesu Almasihu, Ɗan Allah, ke nan.

2 Yadda yake a rubuce a littafin Annabi Ishaya cewa,

“Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,

Wanda zai shirya maka hanya.

3 Muryar mai kira a jeji tana cewa,

Ku shirya wa Ubangiji tarfarki,

Ku miƙe hanyoyinsa.”

4 Yahaya Maibaftisma ya bayyana a jeji, yana wa’azi mutane su tuba a yi musu baftisma domin a gafarta musu zunubansu.

5 Sai duk mutanen ƙasar Yahudiya, da dukan mutanen Urushalima suka yi ta zuwa wurinsa, suna bayyana zunabansu, yana yi musu baftisma a Kogin Urdun.

6 Yahaya kuwa na sanye da tufar gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.

7 Ya yi wa’azi ya ce, “Wani na zuwa bayana wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in sunkuya in ɓalle ba.

8 Ni da ruwa na yi muku baftisma, amma shi da Ruhu Mai Tsarki zai yi muku.”

An Yi wa Yesu Baftisma

9 Sai ya zamana a wannan lokaci Yesu ya zo daga Nazarat ta ƙasar Galili. Yahaya ya yi masa baftisma a Kogin Urdun.

10 Da fitowarsa daga ruwan sai ya ga sama ta dāre, Ruhu yana sauko masa kamar kurciya.

11 Aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai.”

Shaiɗan Ya Gwada Yesu

12 Nan da nan sai Ruhu ya iza shi jeji.

13 Yana jeji har kwana arba’in, Shaiɗan na gwada shi, yana tare da namomin jeji, mala’iku kuma suna yi masa hidima.

Yesu Ya Fara Aiki a Galili

14 To, bayan an tsare Yahaya, sai Yesu ya shigo ƙasar Galili, yana yin bisharar Allah,

15 yana cewa, “Lokaci ya yi, Mulkin Allah ya kusato. Ku tuba, ku gaskata da bishara.”

Yesu Ya Kira Masunta Huɗu

16 Yana wucewa ta bakin Tekun Galili, sai ya ga Bitrus da Andarawas ɗan’uwansa, suna jefa taru a teku, don su masunta ne.

17 Yesu ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.”

18 Nan da nan kuwa suka watsar da tarunansu, suka bi shi.

19 Da ya ci gaba kaɗan, sai ya ga Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan’uwansa Yahaya, suna cikin jirginsu suna gyaran taruna.

20 Nan da nan da ya kira su, suka bar ubansu Zabadi a cikin jirgin tare da ma’aikata, suka bi shi.

Mai Baƙin Aljan

21 Suka shiga Kafarnahum. Ran Asabar kuwa, ya shiga majami’a yana koyarwa.

22 Sun yi mamakin koyarwa tasa, domin yana koya musu da hakikan cewa, ba kamar malaman Attaura ba.

23 Nan take sai ga wani mutum mai baƙin aljan a majami’arsu, yana ihu,

24 yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”

25 Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Yi shiru! Rabu da shi!”

26 Sai baƙin aljanin ya buge shi, jikinsa na rawa, ya yi ihu, ya rabu da shi.

27 Duk suka yi mamaki, har suka tanttambayi juna suna cewa, “Kai, mene ne haka? Tabɗi! Yau ga baƙuwar koyarwa! Har baƙaƙen aljannu ma yake yi wa umarni gabagaɗi, suna kuwa yi masa biyayya!”

28 Nan da nan sai ya shahara a ko’ina duk kewayen ƙasar Galili.

Yesu ya Warkar da Surukar Bitrus

29 Da fitarsu daga majami’a, sai suka shiga gidan su Bitrus da Andarawas, tare da Yakubu da Yahaya.

30 Surukar Bitrus kuwa na kwance tana zazzaɓi, nan da nan suka ba shi labarinta.

31 Sai ya matso, ya kama hannunta, ya tashe ta, zazzaɓin kuwa ya sake ta, har ta yi musu hidima.

Yesu Ya Warkar da Mutane da yawa da Maraice

32 Da magariba, bayan faɗuwar rana, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya, da masu aljannu.

33 Sai duk garin ya haɗu a ƙofar gidan.

34 Ya warkar da marasa lafiya da yawa, masu cuta iri iri, ya kuma fitar wa mutane aljannu da yawa. Bai ko yarda aljannun su yi wata magana ba, domin sun san shi.

Yesu Ya Tafi Yin Wa’azi

35 Da asussuba ya tashi ya fita, ya tafi wani wuri inda ba kowa, ya yi addu’a a can.

36 Sai Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka bi shi.

37 Da suka same shi, suka ce masa, “Duk ana nemanka.”

38 Ya ce musu, “Mu tafi garuruwan da suke gaba, in yi wa’azi a can kuma, domin saboda haka ne na fito.”

39 Ya gama ƙasar Galili duk yana wa’azi a majami’unsu, yana kuma fitar wa mutane aljannu.

Yesu Ya Warkar da Kuturu

40 Wani kuturu ya zo wurinsa, yana roƙonsa, yana durƙusawa a gabansa, yana cewa, “In ka yarda kana da iko ka tsarkake ni.”

41 Da tausayi ya kama Yesu, sai ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce masa, “Na yarda, ka tsarkaka.”

42 Nan take sai kuturtar ta rabu da shi, ya tsarkaka.

43 Ya kwaɓe shi ƙwarai, ya sallame shi nan da nan,

44 ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka saboda tsarkakewarka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”

45 Amma ya tafi, ya shiga sanar da maganar, yana baza labarin al’amarin ko’ina, har ya zamana Yesu bai ƙara shiga wani gari a sarari ba, sai ya zauna a waje a wuraren da ba kowa. Mutane kuwa suka yi ta zuwa wurinsa daga ko’ina.