Shugabanni sun Ƙulla Shawara Gāba da Yesu
1 Sauran kwana biyu a yi Idin Ƙetarewa da idin abinci marar yisti, sai manyan firistoci da malaman Attaura suka nemi hanyar kama Yesu da makirci, su kashe shi,
2 don sun ce, “Ba dai a lokacin idi ba, don kaɗa jama’a su yi hargitsi.”
An Shafi Yesu da Man Ƙanshi a Betanya
3 Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana cin abinci ke nan, sai ga wata mace ta zo da wani ɗan tulu na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tsadar gaske. Sai ta fasa ulun, ta tsiyaye masa man a kā.
4 Waɗansu kuwa da suka ji haushi, suka ce wa juna, “Mene ne na ɓata mai haka?
5 Gama da ma an sayar da shi fiye da dinari ɗari uku, an ba gajiyayyu!” Sai suka hasala da ita, suna gunaguni.
6 Amma Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta. Don me kuke damunta? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa.
7 Kullum kuna tare da gajiyayyu, ko yaushe kuma kuke so, kwa iya yi musu alheri, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.
8 Ta yi iyakacin ƙoƙarinta. Ta shafe jikina da mai gabannin jana’izata.
9 Hakika kuwa ina gaya muku, duk inda za a yi bishara a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa domin tunawa da ita.”
Yahuza Ya Yarda Ya Ba da Yesu
10 Sai Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin sha biyun nan, ya je wurin manyan firistoci don ya bashe shi a gare su.
11 Da suka ji haka suka yi murna, har suka yi alkawarin su ba shi kuɗi. Shi kuwa ya riƙa neman hanyar bashe shi.
Yesu Ya Ci Idin Ƙetarewa tare da Almajiransa
12 A ranar farko ta idin abinci marar yisti, wato ran da aka saba yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa, sai almajiransa suka ce masa, “Ina kake so mu je mu shirya maka cin Idin Ƙetarewa?”
13 Sai ya aiki almajiransa biyu, ya ce musu, “Ku shiga gari, can za ku gamu da wani mutum ɗauke da tulun ruwa, ku bi shi.
14 Duk gidan da ya shiga, ku ce wa maigidan, ‘In ji Malam, ina masaukin da zai ci Idin Ƙetarewa da almajiransa?’
15 Shi kuwa zai nuna muku wani babban soron bene mai kaya a shirye. A nan za ku shirya mana.”
16 Sai almajiran suka tashi, suka shiga gari, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Idin Ƙetarewa.
17 Da magariba ta yi, sai ya zo tare da sha biyun nan.
18 Suna cin abinci ke nan, sai Yesu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni, wanda muke ci tare.”
19 Suka fara baƙin ciki, suna ce masa da ɗaya ɗaya, “Ni ne?”
20 Sai ya ce musu, “Ɗaya daga cikin sha biyun nan ne dai, wanda muke ci ƙwarya ɗaya.
21 Ga shi, Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kuwa, kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”
Cin Jibin Ubangiji
22 Suna cikin cin abinci, sai ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Ungo, wannan jikina ne.”
23 Sai ya ɗauki ƙoƙo kuma, bayan ya yi godiya ga Allah, ya ba su, dukkansu kuwa suka shassha.
24 Sa’an nan ya ce musu, “Wannan jinina ne na tabbatar da alkawari, wanda za a bayar saboda mutane da yawa.
25 Hakika, ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranan nan da zan sha wani sabo a Mulkin Allah.”
26 Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.
Bitrus Zai Yi Musun Sanin Yesu
27 Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe ne, domin a rubuce yake cewa, ‘Zan bugi makiyayi, tumaki kuwa su fasu.’
28 Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.”
29 Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe, ni kam, ba zan yi ba.”
30 Sai Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.”
31 Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi yana cewa, “Ko da za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Dukansu ma haka suka ce.
Yesu Ya Yi Addu’a a Gatsemani
32 Sai suka isa wani wuri, wai shi Getsamani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna nan har in yi addu’a.”
33 Sai ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kuma fara jin wahala gaya, yana damuwa ƙwarai.
34 Sai ya ce musu, “Raina na shan wahala matuƙa, har ma kamar na mutu. Ku dakata nan, ku zauna a faɗake.”
35 Da ya ci gaba kaɗan, sai ya faɗi ƙasa, ya yi addu’a ko ya yiwu a ɗauke masa wannan lokaci.
36 Sa’an nan ya ce, “Ya Abba, Uba, kowane abu mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.”
37 Ya komo ya samu suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Bitrus, barci kake? Ashe, ba za ka iya zama a faɗake ko da sa’a ɗaya ba?
38 Ku zauna a faɗake, ku yi addu’a kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.”
39 Sai ya sāke komawa, ya yi addu’a, yana maimaita maganar dā.
40 Har wa yau kuma ya sāke dawowa, ya samu suna barci, don duk barci ya cika musu ido ƙwarai, sun kuwa rasa abin da za su ce masa.
41 Ya sāke komowa zuwa na uku, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka. Lokaci ya yi. An ba da Ɗan Mutum ga masu zunubi.
42 Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe ni ɗin nan ya matso!”
An Ba da Yesu, an Kama Shi
43 Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabanni ne suka turosu.
44 To, mai bashe shi ɗin nan ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi, ku tafi da shi a rirriƙe.”
45 Da zuwansa kuwa ya zo wurin Yesu, ya ce masa, “Ya shugaba!” sai ya yi ta sumbantarsa.
46 Su kuwa suka danƙe Yesu, suka kama shi.
47 Amma ɗaya daga cikin na tsaye, ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan babban firist sara, ya dauke masa kunne.
48 Sai Yesu ya ce musu, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi?
49 Kowace rana ina tare da ku a Haikalin ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba. Amma an yi haka ne fa domin a cika Littattafai.”
50 Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.
Saurayin da Ya Gudu
51 Sai wani saurayi, daga shi sai mayafi, ya bi shi. Suka kai masa cafka,
52 shi kuwa ya bar musu mayafin, ya gudu huntu.
Yesu a gaban ‘Yan Majalisa
53 Daga nan suka tafi da Yesu wurin babban firist. Duk manyan firistoci da shugabanni da malaman Attaura suka taru a wurinsa.
54 Bitrus kuma ya bi shi daga nesa nesa, har cikin gidan babban firist ɗin, ya zauna cikin dogaran Haikali, yana jin wuta.
55 To, manyan firistoci da ‘yan majalisa duka suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi, amma ba su samu ba.
56 Da yawa kam, sun yi masa shaidar zur, amma bakinsu bai zo ɗaya ba.
57 Daga baya kuma waɗansu suka taso, suka yi masa shaidar zur suka ce,
58 “Mun ji ya ce, wai zai rushe Haikalin nan da mutane suka gina, ya gina wani cikin kwana uku, ba kuwa ginin mutum ba.”
59 Duk da haka dai shaida tasu ba ta zo ɗaya ba.
60 Sai babban firist ya miƙe a tsakiyarsu ya tambayi Yesu ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”
61 Amma yana shiru abinsa, bai amsa kome ba. Sai babban firist ɗin ya sāke tambayarsa, “To, ashe, kai ɗin nan ne Almasihu Ɗan Maɗaukaki?”
62 Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum zaune dama ga Mai Iko, yana kuma zuwa cikin gajimare.”
63 Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Wace shaida kuma za mu nema?
64 Kun dai ji saɓon da ya yi! Me kuka gani?” Duk suka yanke masa shari’a a kan ya cancanci kisa.
65 Waɗansu ma suka fara tattofa masa yau, suka ɗaure masa idanu, suka bubbuge shi, suna ce masa, “Yi annabci!” Dogaran Haikali kuma suka yi ta marinsa.
Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu
66 Bitrus kuwa na ƙasa a filin gida, sai wata baranyar babban firist ta zo.
67 Da ta ga Bitrus na jin wuta, ta zura masa ido, ta ce, “Kai ma, ai, tare kake da Banazaren nan Yesu!”
68 Amma ya musa ya ce, “Ni ban ma san abin da kike faɗa ba, balle in fahimta.” Sai ya fito zaure. Zakara kuwa ya yi cara.
69 Sai baranyar ta gan shi, ta sāke ce wa waɗanda suke tsaitsaye a wurin, “Wannan ma nasu ne.”
70 Amma ya sāke musawa. Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka ce wa Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don Bagalile ne kai.”
71 Sai ya fara la’antar kansa, yana ta rantserantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan da kuke faɗa ba.”
72 Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Yesu ya faɗa masa cewa, “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.” Ko da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.