Yesu a gaban Bilatus
1 Da wayewar gari sai manyan firistoci da shugabanni, da malaman Attaura, da dukkan ‘yan majalisa suka yi shawara. Sai suka ɗaure Yesu, suka tafi da shi, suka ba da shi ga Bilatus.
2 Bilatus ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Yadda ka faɗa.”
3 Sai manyan firistoci suka yi ta kai ƙararsa a kan abubuwa da yawa.
4 Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba ka da wata amsa? Dubi yawan maganganu da suke ba da shaida a kanka!”
5 Yesu dai har yanzu bai yi wata magana ba, har Bilatus ya yi mamaki.
An Hukunta wa Yesu Mutuwa
6 To, a lokacin idi kuwa Bilatus ya saba sakar musu kowane ɗan sarƙa guda da suka roƙa.
7 Akwai wani wai shi Barabbas da yake ɗaure, tare da waɗansu ‘yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin tawayen.
8 Jama’a fa suka matso, suka fara roƙon Bilatus ya yi musu abin da ya saba yi.
9 Sai ya amsa musu, ya ce, “Wato kuna so ne in sakar muku Sarkin Yahudawa?”
10 Don ya gane, saboda hassada ne manyan firistoci suka bashe shi.
11 Amma manyan firistocin suka zuga jama’a, gwamma ya sakar musu Barabbas.
12 Sai Bilatus ya sāke ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da wanda kuke kira Sarkin Yahudawa?”
13 Sai suka sāke yin ihu suka ce, “A gicciye shi!”
14 Bilatus ya ce musu, “Ta wane hali? Wane mugun abu ne ya yi?” Amma su, sai ƙara ɗaga murya suke yi, suna cewa, “A gicciye shi!”
15 Bilatus kuwa da yake yana son ƙayatar da jama’a, ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, ya ba da shi a gicciye shi.
Sojoji Sun Yi wa Yesu Ba’a
16 Sai soja suka tafi da shi cikin fada, wato fadar mai mulkin, suka tara dukkan rundunar soja.
17 Suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura, suka kuma yi wani kambi na ƙaya, suka sa masa a kā.
18 Sai suka fara gaishe shi, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!”
19 Suka riƙa ƙwala masa sanda a ka, suna tattofa masa yau, sa’an nan suka durƙusa, wai suna masa ladabi.
20 Da suka gama yi masa ba’a haka, suka yaye masa alkyabba mai ruwan jar garura, suka sa masa nasa tufafi, suka kai shi waje don su gicciye shi.
An Gicciye Yesu
21 Sai ga wani mai wucewa, wai shi Saminu Bakurane, uban Iskandari da Rufas, yana zuwa daga ƙauye. Suka fa tilasta masa ya ɗauki gicciyen Yesu.
22 Suka kai Yesu wani wuri wai shi Golgota, wato wurin ƙoƙon kai.
23 Suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, amma ya ƙi sha.
24 Sa’an nan suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu, suna kuri’a a kansu, su ga abin da kowa zai samu.
25 Da ƙarfe tara na safe suka gicciye shi.
26 Aka kuma rubuta sanarwar laifinsa sama da shi, wato “Sarkin Yahudawa.”
27 Suka kuma gicciye ‘yan fashi biyu tare da shi, ɗaya dama da shi, ɗaya kuma a hagun. [
28 Wannan shi ne cikar Nassin nan da ya ce, “An lasafta shi a cikin masu laifi.”]
29 Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai, suna cewa, “Ahaf! kai da za ka rushe Haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku,
30 to, sauko daga gicciyen, ka ceci kanka mana!”
31 Haka kuma manyan firistoci da malaman Attaura suka riƙa yi masa ba’a a junansu suna cewa, “Ya ceci waɗansu, ya kuwa kasa ceton kansa,
32 Almasihun nan, Sarkin Isra’ila, yă sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mu gani mu ba da gaskiya.” Waɗanda aka gicciye tare da shi su ma suka zazzage shi.
Mutuwar Yesu
33 Daidai rana tsaka, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.
34 Da ƙarfe ukun sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāna?” wato “Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?”
35 Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, suka ce, “Kun ji yana kiran Iliya.”
36 Sai ɗayansu ya yiwo gudu, ya jiƙo wani soso da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha, yana cewa, “Bari mu gani ko Iliya zai zo ya sauko da shi.”
37 Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, kana ya cika.
38 Sa’an nan labulen da yake cikin Haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa.
39 Sa’ad da jarumi ɗin da yake tsaye yana kallon Yesu, ya ga yadda ya mutu haka, sai ya ce, “Hakika mutumin nan Ɗan Allah ne!”
40 Akwai kuma waɗansu mata da suke hange daga nesa, cikinsu da Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu ƙarami da Yusufu, da kuma Salome,
41 su ne waɗanda suka biyo shi, sa’ad da yake ƙasar Galili, suna yi masa hidima, da kuma mata da yawa da suka rako shi Urushalima.
Jana’izar Yesu
42 La’asar lis, da yake ranar shiri ce, wato gobe Asabar,
43 Yusufu ya zo, mutumin Arimatiya, wani ɗan majalisa mai mutunci, wanda shi ma yake sauraron bayyanar Mulkin Allah, ya yi ƙarfin hali ya shiga wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
44 Bilatus ya yi mamaki ko ya mutu. Sai ya kira jarumin ɗin, ya tambaye shi ko Yesu ya jima da mutuwa.
45 Da ya san haka daga bakin jarumin ɗin sai ya bai wa Yusufu jikin.
46 Sai Yusufu ya sayi likkafanin lilin. Da ya sauko da Yesu, ya sa shi a likkafanin lilin ɗin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe dutse aka yi, ya kuma mirgina wani dutse a bakin kabarin.
47 Maryamu Magadaliya da Maryamu uwar Yusufu sun ga inda aka sa shi.