Almajirai Na Zagar Alkama Ran Asabar
1 A lokacin nan a ran Asabar, Yesu yana ratsa gonakin alkama. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara zagar alkamar suna ci.
2 Amma da Farisiyawa suka ga haka, suka ce masa, “Ka ga! Almajiranka suna yin abin da bai halatta a yi ran Asabar ba.”
3 Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa’ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa?
4 Yadda ya shiga Ɗakin Allah ya ci keɓaɓɓiyar gurasar nan, wadda bai halatta ya ci ba, ko abokan tafiyarsa ma su ci ba, sai dai firistoci kaɗai?
5 Ko kuwa ba ku taɓa karantawa a Attaura ba, yadda a ran Asabar, firistoci a Haikalin sukan keta dokar Asabar, ba tare da yin wani laifi ba kuwa?
6 Ina dai gaya muku, ga wanda ya fi Haikali a nan.
7 Da kun san ma’anar wannan cewa, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba’, da ba ku ga laifin marasa laifi ba.
8 Domin Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”
Mai Shanyayyen Hannu
9 Sai ya ci gaba daga nan ya shiga majami’arsu.
10 Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. Sai suka tambayi Yesu, suka ce, “Ya halatta a warkar a ran Asabar?” Wannan kuwa don su samu su kai ƙararsa ne.
11 Ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da tunkiya, ta faɗa a rami ran Asabar, ba zai kama ta ya fitar da ita ba?
12 Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja? Domin haka ya halatta a yi alheri a ran Asabar.”
13 Sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa. Sai ya koma lafiyayye kamar ɗayan.
14 Amma Farisiyawa suka fita, suka yi shawara a kansa, yadda za su hallaka shi.
Zaɓaɓɓen Bara
15 Da Yesu ya gane haka, ya tashi daga nan. Sai jama’a da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su duka.
16 Sai ya kwaɓe su, kada su bayyana shi.
17 Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,
18 “Ga barana wanda na zaɓa!
Ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai.
Zan sa masa Ruhuna, zai kuma sanar da al’ummai hanyar gaskiya.
19 Ba zai yi husuma ko magana sama sama ba,
Ba kuma wanda zai ji muryarsa tasa a titi.
20 Kyauron da ya tanƙwasa ba zai kakkarye shi ba,
Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba,
Har ya sa gaskiya ta ci nasara.
21 Al’ummai kuma za su sa zuciya ga sunansa.”
Yesu da Ba’alzabul
22 Sai aka kawo masa wani beben makaho mai aljan, ya kuwa warkar da shi, har beben ya yi magana, ya kuma gani.
23 Mutane duk suka yi al’ajabi, suka ce, “Shin, ko wannan shi ne Ɗan Dawuda?”
24 Amma da Farisiyawa suka ji haka sai suka ce, “Ai, da ikon Ba’alzabul sarkin aljannu kawai, wannan yake fitar da aljannu.”
25 Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Ba kuma gari ko gidan da ya rabu a kan gāba, yă ɗore.
26 In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, yā rabu a kan gāba ke nan. To, ta yaya mulkinsa zai ɗore?
27 In kuwa da ikon Ba’alzabul nake fitar da aljannu, to, ‘ya’yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka su ne za su zama alƙalanku.
28 Ni kuwa in da ikon Ruhun Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan.
29 Yaya za a iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum a washe kayansa, in ba an fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin ba? Sa’an nan ne za a iya washe gidansa.
30 Wanda ba nawa ba ne, gāba yake da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.
31 “Don haka ina gaya muku, ā gafarta wa mutane kowane zunubi da saɓo, amma wanda ya saɓi Ruhun, ba za a gafarta masa ba.
32 Kowa ya aibata Ɗan Mutum, ā gafarta masa. Amma wanda ya aibata Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, duniya da lahira.”
Itace da ‘Ya’yansa
33 “Ko dai ku ce itace kyakkyawa ne, ‘ya’yansa kuma kyawawa, ko kuwa ku ce itace mummuna ne, ‘ya’yansa kuma munana. Don itace, da ‘ya’yansa ake gane shi.
34 Ku macizai! Yaya za ku iya yin maganar kirki, alhali kuwa ku mugaye ne? Don abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.
35 Mutumin kirki kam, ta kyakkyawar taskar zuciya tasa yakan yi abin kirki, mugu kuwa, ta mummunar taskar zuciya tasa yakan yi mugun abu.
36 Ina dai gaya muku, a Ranar Shari’a duk hululun da mutum ya yi, za a bincike shi.
37 Maganarka ce za ta kuɓutar da kai, ko kuma ta hukunta ka.”
‘Yan Zamani Suna Neman Alama
38 Waɗansu malaman Attaura da Farisiyawa suka amsa masa suka ce, “Malam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.”
39 Sai ya amsa musu ya ce, “’Yan zamani, mugaye, maciya amana, suke nema su ga wata alama! Amma ba wata alama da za a nuna musu sai dai ta Annabi Yunusa.
40 Wato, kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗan Mutum zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa.
41 A Ranar Shari’a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su kā da su, don sun tuba saboda wa’azin Yunusa. Ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.
42 A Ranar Shari’a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan, ta kā da su, don ta zo ne daga bangon duniya ta ji hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan.
Komawar Baƙin Aljan
43 “Baƙin aljan in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa neman hutu, amma ba ya samu.
44 Sa’an nan sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’ Sa’ad da kuwa ya koma, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, ƙawatacce.
45 Daga nan ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa. Haka zai zamar wa wannan mugun zamani.”
Uwar Yesu da ‘Yan’uwansa
46 Yana cikin magana da taro, sai ga Uwa tasa da ‘yan’uwansa suna tsaye a waje, suna nema su yi magana da shi.
47 Wani ya ce masa, “Ga tsohuwarka da ‘yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”
48 Sai ya amsa wa wanda ya gaya masa, ya ce, “Wace ce tsohuwata, su wane ne kuma ‘yan’uwana?”
49 Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa, ya ce, “Ga nan tsohuwata da ‘yan’uwana nan!
50 Ai, kowa ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so, shi ne ɗan’uwana, shi ne ‘yar’uwata, shi ne kuma tsohuwata.”