Sākewar Kamanninsa
1 Bayan kwana shida sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da ɗan’uwansa Yahaya, ya kai su a kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai.
2 Sai kamanninsa suka sāke a gabansu, fuskarsa ta yi annuri kamar hasken rana, tufafinsa kuma suka yi fari fat suna haske.
3 Ga shi, Musa da Iliya sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu.
4 Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin. In kana so, sai in kafa bukkoki uku a nan, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.”
5 Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”
6 Da almajiran suka ji haka, sai suka faɗi ƙasa, tsoro ya kama su.
7 Sai Yesu ya zo ya taɓa su, ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”
8 Da suka ɗaga kai ba su ga kowa ba, sai Yesu kaɗai.
9 Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”
10 Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, yaya malaman Attaura suke cewa, lalle ne Iliya ya riga zuwa?”
11 Ya amsa ya ce, “Lalle Iliya zai zo ne, zai kuwa raya dukan abubuwa.
12 Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa san shi ne ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗan Mutum zai sha wuya a hannunsu.”
13 Sa’an nan ne almajiran suka gane, ashe, zancen Yahaya Maibaftisma yake yi musu.
Yesu Ya Warkar da Yaro Mai Beben Aljan
14 Da suka isa wurin taro, sai wani mutum ya zo gare shi, ya durƙusa a gabansa, ya ce,
15 “Ya Ubangiji, ka ji tausayin ɗana, yana farfaɗiya, yana shan wuya ƙwarai, sau da yawa yakan faɗa wuta da kuma ruwa.
16 Na kuwa kai shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”
17 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.”
18 Sai Yesu ya tsawata masa, aljanin kuma ya rabu da shi. Nan take yaron ya warke.
19 Sa’an nan almajiran suka zo wurin Yesu a keɓe, suka ce, “Me ya sa mu muka kasa fitar da shi?
20 Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, ‘Kawu daga nan, ka koma can!’, sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku. [
21 Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu’a da azumi.]”
Yesu Ya Sāke Faɗar Irin Mutuwar da Zai Yi
22 Tun suna ƙasar Galili, sai Yesu ya ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane,
23 za su kuwa kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Sai duk tsananin baƙin ciki ya rufe su.
Ba Da Gudunmawar Haikali
24 Da suka zo Kafarnahum masu karɓar rabin shekel na gudunmawar Haikali suka je wurin Bitrus, suka ce, “Malaminku yana ba da gudunmawar?”
25 Ya ce, “I, yakan bayar.” Da ya dawo gida kuma, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani, Bitrus? Wurin wa sarakunan duniya suke karɓar kuɗin fito ko haraji, a wurin ‘ya’yansu, ko kuwa daga wurin waɗansu?”
26 Sa’ad da kuma ya ce, “Daga wurin waɗansu,” sai Yesu ya ce masa, “Wato, ‘ya’yan an ɗauke musu ke nan.
27 Duk da haka, don kada mu ba su haushi, ka je teku ka yi fatsa, kifin da ka fara kamawa kuwa shi za ka ɗauka. In ka buɗe bakinsa za ka sami shekel guda a ciki. To, sai ka ɗauki shekel ɗin nan ka kai musu, wato, nawa da naka.”