Misali na Bikin Aure
1 Yesu ya sāke yi musu magana da misalai ya ce,
2 “Za a kwatanta Mulkin Sama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa biki.
3 Sai ya aiki bayinsa su kirawo waɗanda aka gayyata bikin, amma waɗanda aka gayyatar suka ƙi zuwa.
4 Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku gaya wa waɗanda aka gayyata, “Ga shi, na shisshirya abinci, an yanka shanuna da kiwatattun maruƙana, duk an shirya kome, ku zo bikin mana!” ’
5 Amma suka ƙi kula, suka tafi abinsu, wani ya tafi gona tasa, wani kuma cinikinsa.
6 Sauran kuwa suka kame bayinsa, suka wulaƙanta su, suka kashe su.
7 Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus.
8 Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin fa ya shiryu sosai, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba.
9 Saboda haka ku tafi ƙofofin gari, ku gayyato duk waɗanda kuka samu, su zo bikin.’
10 Sai bayin suka yi ta bin titi titi, suka tattaro duk waɗanda suka samu, mugaye da nagargaru duka, har wurin bikin ya cika maƙil da baƙi.
11 “Da sarki ya shigo ganin baƙin sai ya ga wani mutum a can wanda bai sa riga irin ta biki ba.
12 Sai ya ce masa, ‘Malam, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba?’ Mutumin kuwa ya rasa ta cewa.
13 Sai sarki ya ce wa barorinsa, ‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baƙi.’
14 Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”
Biyan Haraji ga Kaisar
15 Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa.
16 Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai.
17 To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?”
18 Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai!
19 Ku nuna mini kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari.
20 Yesu ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?”
21 Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa’an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”
22 Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.
Tambaya a kan Tashin Matattu
23 A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya,
24 suka ce, “Malam, Musa dai ya ce, ‘In mutum ya mutu, bai bar na baya ba, sai lalle ɗan’uwansa ya auri matar, ya haifa wa ɗan’uwansa ‘ya’ya.’
25 To, an yi waɗansu ‘yan’uwa maza bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, da ya rasu, da yake bai haifu kuma ba, sai ya bar wa ɗan’uwansa matarsa.
26 Haka ya faru ga na biyun da na ukun, har ya kai kan na bakwai ɗin.
27 Bayansu duka sai matar ta rasu.
28 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu, su bakwai ɗin? Don duk sun aure ta.”
29 Amma Yesu ya amsa musu ya ce, “Kun ɓăta ne, domin ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba.
30 Domin a tashin matattu, ba a aure, ba a aurarwa, sai dai kamar mala’ikun da suke Sama ake.
31 Game da tashin matattu, ashe, ba ku taɓa karanta abin da Allah ya ce muku ba? cewa,
32 ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.’ Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.”
33 Da jama’a suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
Umarni Mafi Girma
34 Amma da Farisiyawa suka ji ya ƙure Sadukiyawa, suka taru.
35 Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Attaura, ya yi masa tambaya, yana gwada shi, ya ce,
36 “Malam, wane umarni ne mafi girma a cikin Attaura?”
37 Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.
38 Wannan shi ne babban umarni na farko.
39 Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.’
40 A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.”
Tambaya a kan Ɗan Dawuda
41 Tun Farisiyawa suna tare gu ɗaya, sai Yesu ya yi musu tambaya,
42 ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.”
43 Ya ce musu, “To, yaya kuwa Dawuda, ta ikon Ruhu, ya ce da shi Ubangiji? Har ya ce,
44 ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
Zauna a damana,
Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’
45 Tun da Dawuda ya kira shi Ubangiji ne, to, ƙaƙa zai zama ɗansa?”
46 Ba kuwa wanda ya iya tanka masa. Daga ran nan kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.