MAT 6

Koyarwar Yesu a kan Ba Da Sadaka

1 “Ku yi hankali kada ibadarku ta zama ta ganin ido. Domin in kun yi haka, ba za ku sami sakamako wurin Ubanku da yake a Sama ba.

2 “Wato, in za ka yi sadaka, kada ka yi kwakwazo yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan hanya don dai mutane su yabe su. Gaskiya nake faɗa muku, sun sami iyakar ladarsu ke nan.

3 Amma in kana yin sadaka, kada hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama yake yi,

4 domin sadakarka tă zama a asirce, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”

Koyarwar Yesu a kan Addu’a

5 “In za ku yi addu’a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu’a a tsaye a majami’u da kan hanya, wai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun sami iyakar ladansu.

6 Amma in za ka yi addu’a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.

7 “In kuwa kuna addu’a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al’ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu.

8 Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.

9 Saboda haka sai ku yi addu’a kamar haka,

‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama,

A kiyaye sunanka da tsarki.

10 Mulkinka yă zo,

A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.

11 Ka ba mu abincinmu na yau.

12 Ka gafarta mana laifofinmu,

Kamar yadda mu ma muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.

13 Kada ka kai mu wurin jaraba,

Amma ka cece mu daga Mugun.’

14 Domin in kun yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku na Sama zai yafe muku.

15 In kuwa ba ku yafe wa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.”

Koyarwar Yesu a kan Azumi

16 “In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, wai don mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan.

17 Amma in kana azumi, ka shafa mai a ka, ka kuma wanke fuska,

18 don kada mutane su ga alama kana azumi, sai dai Ubanku da yake ɓoye ya gani. Ubanku kuma da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”

Tara Dukiya a Sama

19 “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda ɓarayi kuma suke karyawa su yi sata.

20 Sai dai ku tara wa kanku dukiya a Sama, inda ba asu da tsatsa da za su ɓata, inda kuma ba ɓarayin da za su karya su yi sata.

21 Domin kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”

Fitilar Jiki

22 “Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka ma sai ya cika da haske.

23 In kuwa idonka da lahani, duk jikinka sai ya cika da duhu. To, in hasken da yake gare ka duhu ne, ina misalin yawan duhun!”

Bauta wa Allah ko Dukiya

24 “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu; ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”

Damuwa da Alhini

25 “Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu a kan rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuwa jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe, rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba?

26 Ku dubi dai tsuntsaye. Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa kuma tarawa a rumbuna, amma kuwa Ubanku na Sama na ci da su. Ashe, ko ba ku fi martaba nesa ba?

27 Wane ne a cikinku, don damuwarsa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa?

28 To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin jeji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi,

29 duk da haka ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba.

30 To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!

31 Don haka kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ ko, ‘Me za mu sha?’ ko kuwa, ‘Me za mu sa?’

32 Ai, al’ummai ma suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka.

33 Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.

34 “Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe ta Allah ce. Wahalce-wahalcen yau ma sun isa wahala.”