Kada Ku Ɗora wa Kowa Laifi
1 “Kada ku ɗora wa kowa laifi, don kada a ɗora muku.
2 Don da irin hukuncin da kuka zartar, da shi za a zartar muku. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.
3 Don me kake duban ɗan hakin da yake idon ɗan’uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba?
4 Ko kuwa yaya za ka iya ce wa ɗan’wanka, ‘Bari in cire maka ɗan hakin daga idonka,’ alhali kuwa da gungume a naka ido?
5 Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake idonka tukuna, sa’an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan’uwanka.
6 “Kada ku ba karnuka abin da yake tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu’ulu’unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.”
Ku Roƙa, Ku Nema, Ku Ƙwanƙwasa
7 “Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.
8 Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.
9 To, wane ne a cikinku, ɗansa zai roƙe shi gurasa, ya ba shi dutse?
10 Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji?
11 To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba ‘ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?
12 Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”
Ƙunƙuntar Ƙofa
13 “Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa hallaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa.
14 Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”
Akan Gane Itace ta ‘Ya’yansa
15 “Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa.
16 Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?
17 Haka kowane itacen kirki yakan haifi kyawawan ‘ya’ya. Mummunan itace kuwa yakan haifi munanan ‘ya’ya.
18 Kyakkyawan itace ba dama ya haifi munanan ‘ya’ya. Haka kuma mummunan itace ba dama ya haifi kyawawan ‘ya’ya.
19 Duk itacen da ba ya ‘ya’ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta.
20 Don haka, da irin aikinsu za a gane su.”
Ban Taɓa Saninku ba
21 “Ba duk mai ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so.
22 A ranar nan da yawa za su ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci da sunanka ba? Ba mu fitar da aljannu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al’ajabi masu yawa da sunanka ba?’
23 Sa’an nan zan ce musu, ‘Ni ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu yin mugun aiki.’ ”
Kafa Harsashin Gini Iri Biyu
24 “Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā.
25 Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, iska ta taso ta bugi gidan, amma bai faɗi ba, domin an gina shi a kan fā ne.
26 Kowa ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta kuma ba, za a misalta shi da wawan mutum, wanda ya gina gidansa a kan rairayi.
27 Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, sai iska ta taso ta bugi gidan har ya rushe, mummunar ragargajewa kuwa!”
Hakikancewar Yesu
28 Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa,
29 domin yana koya musu da hakikancewa, ba kamar malamansu na Attaura ba.