Yesu Ya Warkar da Kuturu
1 Da ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawan gaske suka bi shi.
2 Sai ga wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.”
3 Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take kuturtarsa ta warke.
4 Sai Yesu ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”
Yesu Ya Warkar da Yaron Wani Jarumi
5 Yana shiga Kafarnahum ke nan, sai wani jarumi ya zo gunsa ya roƙe shi,
6 ya ce, “Ya Ubangiji, yarona na kwance a gida, ya zama shanyayye, yana shan azaba ƙwarai.”
7 Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.”
8 Sai jarumin, ya ce, “Ya Ubangiji, ban isa har ka zo gidana ba, amma sai ka yi magana kawai, yarona kuwa zai warke.
9 Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, sai in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.”
10 Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya muku, ko a cikin Isra’ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.
11 Ina kuma gaya muku, da yawa za su zo daga gabas da yamma su zauna cin abinci tare da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a Mulkin Sama,
12 ‘ya’yan Mulki kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.”
13 Sai Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka, ya zama maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi.” Nan take yaronsa ya warke.
Yesu Ya Warkar da Surukar Bitrus
14 Da Yesu ya shiga gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzaɓi.
15 Sai ya taɓa hannunta, zazzaɓin ya sake ta, ta kuma tashi ta yi masa hidima.
Yesu Ya Warkar da Mutane da Yawa da Maraice
16 Da maraice ya yi, sai suka kakkawo masa masu aljannu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljannun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.
17 Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa, “Da kansa ya ɗebe rashin lafiyarmu, ya ɗauke cucecucenmu.”
Masu Cewa, Za Su Bi Yesu
18 To, da Yesu ya ga taro masu yawan gaske sun kewaye shi, sai ya yi umarni a koma wancan hayi.
19 Sai wani malamin Attaura ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.”
20 Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da sheƙunan, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”
21 Sai ɗaya daga almajiran ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”
22 Amma Yesu ya ce masa, “Bi ni. Bari matattu su binne ‘yan’uwansu matattu.”
Yesu Ya Tsawata wa Hadiri
23 Da ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi.
24 Sai ga wani babban hadiri ya taso a teku, har raƙuman ruwa suka fara shan kan jirgin, amma yana barci.
25 Sai almajiransa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ya Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!”
26 Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa’an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit!
27 Mutanen suka yi al’ajabi, suka ce, “Wane irin mutum ne wannan, wanda har iska da ruwan teku ma suke masa biyayya?”
Warkar da Masu Aljannu na Garasinawa
28 Da ya isa wancan hayi a ƙasar Garasinawa, mutum biyu masu aljannu suka fito daga makabarta suka tarye shi. Don kuwa su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bi ta wannan hanya.
29 Sai suka ƙwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”
30 Nesa kuma kaɗan akwai wani babban garken alade na kiwo.
31 Sai aljannun suka roƙe shi, suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladen nan.”
32 Ya ce musu, “To, ku je.” Sai suka fita, suka shiga aladen. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka faɗa tekun, suka hallaka a ruwa.
33 Masu kiwon aladen suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin kome da kome, da kuma abin da ya auku ga masu aljannun.
34 Sai ga duk jama’ar garin sun firfito su taryi Yesu. Da suka gan shi, sai suka roƙe shi ya bar musu ƙasarsu.