1 Ubangiji ya yi magana da Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da na Hezekiya, sarakunan Yahuza. Ya yi masa magana a kan Samariya da Urushalima.
Makoki don Samariya da Urushalima
2 Dukanku ku ji, ku al’ummai!
Ki kasa kunne, ya duniya, da dukan
abin da yake cikinki.
Bari Ubangiji Allah
Daga Haikalinsa mai tsarki ya zama
shaida a kanku.
3 Ga shi, Ubangiji yana fitowa daga
wurin zamansa,
Zai sauko, ya taka kan tsawawan
duwatsun duniya.
4 Duwatsu za su narke a
ƙarƙashinsa,
Kwaruruka za su tsattsage kamar
kakin zuma a gaban wuta,
Kamar ruwa yana gangarowa daga
tsauni.
5 Duk wannan kuwa saboda laifin
Yakubu ne,
Da laifin Isra’ila.
Mene ne laifin Yakubu?
Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin
da ake yi a Samariya ba?
Mene ne kuma laifin Yahuza?
Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin
da ake yi a Urushalima ba?
6 “Domin haka zan mai da Samariya
jujin kufai a karkara,
Wurin dasa kurangar inabi.
Zan zubar da duwatsunta a cikin
kwari,
In tone harsashin gininta.
7 Za a farfashe dukan siffofinta na
zubi,
Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta,
Zan lalatar da gumakanta duka,
Gama ta wurin karuwanci ta samo
su,
Ga karuwanci kuma za su koma.”
8 Mika ya ce, “Saboda wannan zan yi
baƙin ciki, in yi kuka,
Zan tuɓe, in yi tafiya huntu.
Zan yi kuka kamar diloli,
In yi baƙin ciki kamar jiminai.
9 Gama raunin Samariya, ba ya
warkuwa,
Gama ya kai Yahuza,
Ya kuma kai ƙofar jama’ata a
Urushalima.”
10 Kada a faɗe shi a Gat,
Sam, kada a yi kuka.
Yi birgima cikin ƙura a Bet-leyafra.
11 Ku mazaunan Shafir, ku wuce
abinku da tsiraici da kunya.
Mazaunan Za’anan ba su tsira ba.
Bet-ezel ta yi kururuwa, “Zai
tumɓuke harasashin gininki.”
12 Mutanen Marot sun ƙosa su ga
alheri,
Amma masifa ta zo ƙofar
Urushalima daga wurin Ubangiji.
13 Ku mutanen Lakish, ku ɗaura wa
dawakai karusai,
Gama ku kuka fara yin zunubi a
Sihiyona,
Gama an iske laifofin Isra’ila
cikinku.
14 Domin haka sai ku ba Moreshet-gat
guzuri,
Mutanen Akzib za su yaudari
sarakunan Isra’ila.
15 Ku mazaunan Maresha, Ubangiji zai
kawo wanda zai ci ku da yaƙi,
Darajar Isra’ila za ta shiga
Adullam.
16 Ku aske kanku saboda ƙaunatattun
‘ya’yanku.
Ku yi wa kanku ƙwaƙwal kamar
ungulu,
Gama ‘ya’yanku za su tafi bautar
talala.