Lalacewar Isra’ila
1 Tawa ta ƙare, gama na zama
kamar lokacin da aka gama
tattara amfanin gona,
Kamar lokacin da aka gama kalar
‘ya’yan inabi,
Ba nonon inabi da za a tsinka, a ci,
Ba kuma ‘ya’yan ɓaure da suka
harba wanda raina yake so.
2 Mutanen kirki sun ƙare a duniya,
Ba nagarta a cikin mutane.
Dukansu suna kwanto don su zub da
jini.
Kowa yana farautar ɗan’uwansa da
tarko.
3 Sun himmantu su aikata abin da yake
mugu da hannuwansu.
Sarki da alƙali suna nema a ba su
hanci,
Babban mutum kuma yana faɗar son
zuciyarsa,
Da haka sukan karkatar da zance.
4 Mutumin kirkinsu kamar ƙaya yake,
Mai gaskiyarsu kuwa kamar shingen
ƙaya yake.
Ranar da kuka sa mai tsaro,
A ran nan za a aukar muku da
hukunci.
Yanzu ruɗewarku ta zo,
5 Kada ka dogara ga maƙwabcinka,
Kada kuma ka amince da abokinka.
Ka kuma kame bakinka daga
matarka
Wadda take kwance tare da kai.
6 Gama ɗa yana raina mahaifi,
‘Ya kuma tana tayar wa
mahaifiyarta,
Matar ɗa kuma tana gāba da
surukarta,
Mutanen gidan mutum su ne
maƙiyansa.
Ubangiji Zai Kawo Haske da Ceto
7 Amma ni zan kafa ido ga Ubangiji,
Zan jira ceton Allahna,
Allahna zai ji ni.
8 Ya maƙiyina, kada ka yi murna a
kaina,
Gama sa’ad da na fāɗi, zan tashi
kuma.
Sa’ad da na zauna cikin duhu,
Ubangiji zai haskaka ni.
9 Zan ɗauka fushin Ubangiji ne,
Gama na yi masa zunubi,
Sai lokacin da ya ji da’awata,
Har ya yanke mini shari’a.
Zai kawo ni zuwa wurin haske,
Zan kuwa ga cetonsa.
10 Sa’an nan maƙiyina wanda suke ce mini,
“Ina Ubangiji Allahnka?”
Zai gani, ya kuma ji kunya.
Idanuna za su gan shi lokacin da aka
tattake shi
Kamar taɓo a titi.
11 Za a faɗaɗa iyakarka
A ranar da za a gina garunka.
12 A waccan rana mutane za su zo
wurinka,
Daga Assuriya har zuwa Masar,
Daga Masar zuwa Kogin Yufiretis,
Daga teku zuwa teku, daga dutse
zuwa dutse.
13 Duniya kuwa za ta zama kufai,
Saboda mazaunan da suke cikinta,
Saboda hakkin ayyukansu.
Juyayin Ubangiji a kan Isra’ila
14 Sai ka yi kiwon mutanenka da
sandanka,
Wato garken mallakarka,
Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi
A tsakiyar ƙasa mai albarka.
Bari su yi kiwo cikin Bashan da
Gileyad
Kamar a kwanakin dā.
15 “Zan nuna muku abubuwa masu
banmamaki,
Kamar a kwanakin da kuka fito
ƙasar Masar.”
16 Al’umman duniya za su gani,
Su kuwa ji kunyar ƙarfinsu duka.
Za su sa hannuwansu a baka,
Kunnuwansu za su kurmance.
17 Za su lashi ƙura kamar maciji da
abubuwa masu rarrafe,
Za su fito da rawar jiki daga wurin
maɓuyarsu,
Da tsoro za su juyo wurin Ubangiji
Allahnmu,
Za su ji tsoronka.
18 Akwai wani Allah kamarka, mai yafe
mugunta,
Mai kawar da laifin ringin
gādonsa?
Ba ya riƙon fushi har abada, gama
shi mai alheri ne.
19 Zai sāke jin juyayinmu,
Ya tattake muguntarmu a ƙarƙashin
ƙafafunsa.
Za ka jefar da zunubanmu a cikin
zurfin teku.
20 Za ka nuna wa Yakubu aminci,
Ga Ibrahim kuma madawwamiyar
ƙauna,
Kamar yadda ka rantse wa
kakanninmu
Tun a zamanin dā.