Gaisuwa
1 Daga Bulus, bawan Yesu Almasihu, manzo kirayayye, keɓaɓɓe domin yin bisharar Allah,
2 wadda Allah ya yi alkawari tun dā, ta bakin annabawansa a cikin Littattafai masu tsarki.
3 Bishara ɗin nan a kan Ɗansa ce, Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ga jiki shi zuriyar Dawuda ne,
4 amma ga tsarkinsa na ruhu shi Ɗan Allah ne, da iko aka ayyana shi haka ta wurin tashinsa daga matattu.
5 Ta wurinsa ne muka sami alheri da kuma manzanci, saboda sunansa dukan al’ummai su gaskata su yi biyayya,
6 a cikinsu kuma har da ku da kuke kirayayyun Yesu Almasihu.
7 Daga Bulus zuwa ga dukan ƙaunatattun Allah da kuke a Roma, tsarkaka kirayayyu.
Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.
Nufin Bulus Ya Ziyarci Roma
8 Da farko dai ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko’ina a duniya.
9 Domin kuwa Allah, wanda nake bauta wa a ruhuna ta yin bisharar Ɗansa, shi ne mashaidina a kan yadda kullum ba na fasa ambatonku a cikin addu’ata,
10 ina addu’a, ko ta ƙaƙa, da yardar Allah, a yanzu kam, in sami arzikin zuwa wurinku.
11 Domin ina ɗokin ganinku, in ni’imta ku da wata baiwa ta ruhu, domin ku ƙarfafa.
12 Wato ni da ku, mu ƙarfafa juna ta bangaskiyarmu, tawa da taku.
13 Ina so ku sani ‘yan’uwa, na sha ɗaura niyyar zuwa wurinku, ko da yake har yanzu ba a yardar mini ba, domin ku ma in sami amfani a gare ku, kamar yadda na samu a cikin al’ummai.
14 Akwai hakkin Helenawa, da na bare, da na masu ilimi, da na jahilai duka a kaina.
15 Saboda haka a gwargwadon iyawata, ina da himma ku ma in yi muku bisharar, ku da kuke a Roma.
Ikon Bishara
16 Gama ba na jin kunyar bishara, domin ita ce ikon Allah mai kai kowane mai ba da gaskiya ga samun ceto, Yahudawa da fari, sa’an nan kuma al’ummai.
17 Gama bishara ɗin ta bayyana wata hanyar samun adalci a gaban Allah, hanyar nan kuwa ta bangaskiya ce, tun daga farko har zuwa ƙarshe, yadda yake a rubuce cewa, “Wanda yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.”
Laifin ‘Yan Adam
18 Gama ana bayyana fushin Allah daga Sama, a kan dukan rashin bin Allah, da aikin mugunta na mutanen da suke danne gaskiya, ta aikin muguntarsu,
19 Domin abin da za a iya sani a game da Allah a bayyane yake a gare su, gama Allah ne ya bayyana musu shi.
20 Gama tun daga halittar duniya al’amuran Allah marasa gănuwa, wato ikonsa madawwami, da allahntakarsa, sun fahimtu sarai, ta hanyar abubuwan da aka halitta kuma ake gane su. Saboda haka mutane sun rasa hanzari.
21 Domin kuwa ko da yake sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta.
22 Suna da’awa cewa, su masu hikima ne, sai suka zama wawaye.
23 Sun sauya ɗaukakar Allah marar mutuwa da misalin siffar mutum mai mutuwa, da ta tsuntsaye, da ta dabbobi, da kuma ta masu jan ciki.
24 Saboda haka Allah ya sallama su ga rashin tsarkaka ta mugayen sha’awace-sha’awacensu, har su wulakanta jikinsu a junansu,
25 saboda sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, har yi wa halitta ibada, sun kuma bauta mata, sun ƙi su yi wa Mahalicci, shi wanda yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin.
26 Don haka Allah ya sallama su ga mugayen sha’awace-sha’awace masu banƙyama, har matansu suka sauya ɗabi’arsu ta halal, da wadda take ta haram.
27 Haka kuma maza suka bar ma’amalarsu ta halal da mata, jarabar juna ta ɗebe su, maza da maza suna aikata rashin kunya, suna jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.
28 Tun da yake sun ƙi su yarda su san Allah, Allah ya sallama su ga halin banza, su aikata abin kunya.
29 Su masu aikata rashin adalci ne ƙwarai, da mugunta, da kwaɗayi, da ƙeta. Masu hassada ne, da kisankai, da jayayya, da ha’inci, da kuma nukura gaya matuƙa. Macizan ƙaiƙayi ne,
30 da masu yanke, da maƙiyan Allah, da masu cin mutunci, da masu girmankai, da masu ruba, da masu haddasa mugunta, da marasa bin iyaye,
31 da marasa fahimta, da masu ta da alkawari, da marasa ƙauna, da marasa tausayi.
32 Waɗannan kuwa ko da yake sun san shari’ar Allah cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, sun cancanci mutuwa, duk da haka, ba aikata su kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon masu yinsu.