1 Bari kowa yă yi biyayya ga mahukunta. Gama ba wani iko sai da yardar Allah. Mahukuntan da suke nan kuwa naɗin Allah ne.
2 Saboda haka duk wanda ya yi wa mahukunta tsayayya, ya yi wa umarnin Allah ke nan, masu yin tsayayyar nan kuwa za a yi musu hukunci.
3 Don kuwa mahukunta ba abin tsoro ba ne ga masu aiki nagari, sai dai ga masu mugun aiki. Kana so kada ka ji tsoron mahukunci? To, sai ka yi nagarta, sai kuwa ya yaba maka.
4 Domin shi bawan Allah ne, don kyautata zamanka. Amma in kai mai mugun aiki ne, to, ka ji tsoro, don ba a banza yake riƙe da takobi ba. Ai, shi bawa ne na Allah, mai sāka wa mugu da fushi.
5 Saboda haka wajibi ne ka yi biyayya, ba domin gudun fushi kaɗai ba, amma domin lamiri kuma.
6 Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, don su mahukunta ma’aikata ne na Allah, suna kuma yin wannan aiki a koyaushe.
7 Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu, masu kuɗin fito, kuɗinsu na fito, waɗanda suka cancanci ladabi, ladabi, waɗanda suka cancanci girmamawa, girmamawa.
8 Kada hakkin kowa ya zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Shari’a ke nan.
9 Umarnan nan cewa, “kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi,” da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
10 Ƙauna ba ta cutar maƙwabci saboda haka ƙauna cika Shari’a ce.
11 Ga shi kuma, kun dai san irin zamanin da muke a ciki, ai, lokaci ya riga ya yi da za ku farka daga barci. Gama yanzu mun fi kusa da ceton nan namu a kan sa’ad da muka fara ba da gaskiya.
12 Dare fa ya ƙure, gari ya kusa wayewa. Sai mu watsar da ayyukan duhu, mu yi ɗamara da kayan ɗamara na haske.
13 Mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa, ko fasikanci da fajirci, ko jayayya da kishi ba.
14 Amma ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutuntaka, don biye wa muguwar sha’awarsa.