1 To, ina fifikon Bayahude? Ko kuma ina fa’idar kaciya?
2 Ai kuwa, akwai ƙwarai, ta kowace hanya. Da farko dai, Yahudawa su ne aka amince wa a game da zantuttukan Allah.
3 To, ƙaƙa ke nan in waɗansu sun ci amanar nan? Sai cin amanarsu ya shafe cikar alkawarin Allah?
4 A’a, ko kusa! A dai tabbata Allah mai gaskiya ne, ko da yake kowane mutum maƙaryaci ne, yadda yake a rubuce cewa,
“Don maganarka tă tabbatar da adalcinka,
Ka kuma yi rinjaye in an binciki al’amarinka.”
5 In kuwa rashin adalcinmu shi ne yake nuna adalcin Allah a fili, me za mu ce? in Allah ya hore mu, ya yi rashin adalci ke nan? (Misali nake yi kawai.)
6 A’a, ko kusa! To, in da haka ne, ta ƙaƙa Allah zai yi wa duniya shari’a?
7 In kuwa, a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka kara ɗaukaka shi, to, don me har yanzu ake hukunta ni a kan ni mai zunubi ne?
8 In haka ne, ba sai mu yi ta yin mugun aiki don ya zama sanadin nagarta ba? Kamar yadda dai waɗansu suke mana yanke, cewa haka muke faɗa. Hukuncin da za a yi wa irin waɗannan kuwa daidai ne.
Babu Mai Adalci
9 To, ƙaƙa? Mu Yahudawa mun fi sauran ne? A’a, ko kaɗan! Don dā ma mun ɗora wa Yahudawa da al’ummai laifi, cewa dukkansu zunubi yana iko da su.
10 Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya,
11 Babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.
12 Duk sun bauɗe, sun zama marasa amfani baki ɗaya,
Babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda ɗaya.”
13 “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗen kabari ne,
Maganarsu ta yaudara ce.”
“Masu ciwon baki ne.”
14 “Yawan zage-zage da ɗacin baki gare su.”
15 “Masu hanzarin zub da jini ne,
16 Ta ko’ina suka bi sai hallaka da baƙin ciki,
17 Ba su kuma san hanyar salama ba.”
18 “Babu tsoron Allah a cikin sha’aninsu sam.”
19 To, mun sani duk abin da Shari’a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take.
20 Ai, ba wani ɗan adam da zai sami kuɓuta ga Allah ta kiyaye ayyukan Shari’a, tun da yake ta Shari’a ne mutum yake ganin laifinsa.
Adalci ta Wurin Bangaskiya
21 A yanzu, ba kuwa a game da shari’a ba, an bayyana wata hanyar samun adalcin Allah, wadda ma Attaura da littattafan annabawa suke yi wa shaida.
22 Adalcin nan na Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya ga Yesu Almasihu, na masu ba da gaskiya ne dukka, ba kuwa wani bambamci,
23 gama ‘yan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah.
24 Amma ta wurin alherin da Allah ya yi musu kyauta, sun sami kuɓuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi.
25 Allah kuwa ya ayyana Yesu Almasihu ya zama hadayar sulhu, ta wurin ba da gaskiya ga jininsa. Allah kuwa ya yi haka domin yă nuna adalcinsa ne, domin dā saboda haƙurinsa ya jingine zunuban da aka gabatar,
26 domin a nuna adalcinsa a wannan zamani, wato a bayyana shi kansa mai adalci ne, mai kuɓutar da duk mai gaskatawa da Yesu kuma.
27 To, ina kuma fariyarmu ta shiga? Ina kuwa! Ta wace hanya aka kawar da ita? Ta aikin lada? A’a, sai dai ta hanyar bangaskiya.
28 Domin mun amince, cewa ta bangaskiya ne mutum yake kuɓuta, ba ta kiyaye ayyukan Shari’a ba.
29 Wato Allah, Allahn Yahudawa ne kurum? Ashe, ba na al’ummai ba ne kuma? Hakika na al’ummai ne ma,
30 tun da yake Allah ɗaya ne, zai kuwa kuɓutar da masu kaciya ta wurin bangaskiya, marasa kaciya ma ta wannan bangaskiya.
31 Wato mun soke Shari’a ke nan ta bangaskiyar nan? A’a, ko kusa! Sai tabbatar da ita muka yi.