Gaisuwa
1 Daga Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, saboda bangaskiyar zaɓaɓɓun Allah, da kuma inganta sanin gaskiyar ibadarmu,
2 duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil’azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,
3 ya kuwa bayyana maganarsa a lokacin da ya ƙayyade, ta wa’azin da shi Allah Mai Cetonmu ya amince mini in yi, bisa ga umarninsa,
4 zuwa ga Titus, ɗana na hakika ta wajen bangaskiyarmu mu duka.
Alheri da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Mai Cetonmu su tabbata a gare ka.
Aikin Titus a Karita
5 Wannan shi ya sa na bar ka a Karita, musamman domin ka ƙarasa daidaita al’amuran da suka saura, ka kuma kafa dattawan ikkilisiya a kowane gari, kamar yadda na nushe ka,
6 sai wanda ya kasance marar abin zargi, mai mace ɗaya, wanda ‘ya’yansa suke masu ba da gaskiya, waɗanda ba a zarginsu da aikin masha’a ko na kangara.
7 Lalle ne kuwa, kowane mai kula da ikkilisiya, da yake shi mai riƙon amana saboda Allah ne, yă zama marar abin zargi, ba mai taurinkai ba, ko mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai saurin dūka, ko mai kwaɗayin ƙazamar riba.
8 Amma yă kasance mai yi wa baƙi alheri, mai son abu nagari, natsattse, mai kirki, tsarkakakke, mai kamunkai,
9 mai riƙe da tabbatacciyar maganar nan kankan, daidai yadda aka koya masa, domin yă iya ƙarfafa wa waɗansu zuciya da sahihiyar koyarwa, ya kuma ƙaryata waɗanda suka yi musunta.
10 Don kuwa akwai kangararrun mutane da yawa, da masu surutan banza, da masu ruɗi, tun ba ma ɗariƙar masu kaciyar nan ba.
11 Lalle ne a kwaɓe su, tun da yake suna jirkitar da jama’a gida gida, ta wurin koyar da abin da bai kamata ba, don neman ƙazamar riɓa.
12 Wani annabi na Karitawa ya ce, “Karitawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye, haɗamammu.”
13 Shaidar nan tasa kuwa gaskiya ce. Saboda haka, dai ka tsawata musu da gaske, domin su zama sahihai a wajen bangaskiya,
14 a maimakon su mai da hankali ga almarar Yahudawa, ko kuwa dokokin mutane masu ƙin gaskiya.
15 Ga masu tsarkin rai duk al’amarinsu mai tsarki ne, marasa tsarkin rai kuwa marasa ba da gaskiya, ba wani al’amarinsu da yake mai tsarki, da zuciyarsu da lamirinsu duka marasa tsarki ne.
16 Suna cewa sun san Allah, amma suna sāɓa masa ta wurin aikinsu. Abin ƙyama ne su, kangararru, ko kaɗan ba su da wani amfani a wajen yin aiki nagari.