Ango Ya Yabi Amarya
1 Kyakkyawa ce ke ƙaunatacciyata.
Idonki kamar na kurciya, suna haskakawa daga cikin lulluɓi.
Gashinki yana zarya kamar garken awaki
Da yake gangarowa daga tuddan Gileyad.
2 Haƙoranki farare fat kamar tunkiyar da aka yi mata sausaya,
Aka yi mata wanka nan da nan.
Ba giɓi, suna nan shar.
An jera su tantsai.
3 Leɓunanki ja wur kamar kin shafa jan-baki.
Maganarki tana faranta zuciya.
Kumatunki suna haske bayan lulluɓi.
4 Wuyanki kamar hasumiyar Dawuda yake, kewayayye sumul sumul,
Inda aka rataye garkuwoyi dubu na jarumawa.
5 Mamanki kamar bareyi biyu ne,
Wato tagwayen barewa, suna kiwo cikin furen bi-rana.
6 Har iskar safiya ta huro,
Duhu kuma ya kawu,
Zan zauna a kan tudun mur,
Wato tudun kayan ƙanshi.
7 Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata,
Ba wanda zai kushe ki!
8 Amaryata, ki taho daga Dutsen Lebanon,
Taho daga Lebanon.
Ki taho daga ƙwanƙolin Dutsen Amana,
Da Dutsen Senir da Harmon,
Inda zakuna da damisoshi suke zaune.
9 Kallon idonki, budurwata, amaryata,
Da duwatsun da suke wuyanki
Sun sace zuciyata.
10 Ƙaunarki abar murna ce, ya budurwata, amaryata!
Ƙaunarki ta fi ruwan inabi.
Ƙanshinki ya fi kowane irin turare ƙanshi.
11 Zaƙin leɓunanki kamar zuma ne, ya budurwata,
A gare ni harshenki madara ne da zuma.
Tufafinki suna ƙanshi kamar turaren da yake cikin Dutsen Lebanon.
12 Budurwata, amaryata, ke asirtaccen lambu ce,
Lambu mai katanga, asirtacciyar maɓuɓɓuga.
13 Shuke-shuke suna girma sosai.
Suna girma kamar gonar itatuwan rumman.
Suna ba da ‘ya’ya mafi kyau
Da kayan shafe-shafe kamar su lalle da nardi.
14 Nardi, da asfaran, da kalamus, da kirfa,
Da dukan itatuwan da suke ba da kayan ƙanshi,
Da mur, da aloyes, da dukan turare mafi ƙanshi.
15 Maɓuɓɓugai suna ba lambun ruwa, ruwan rafuffuka suna gudu,
Ƙoramu suna bulbulo ruwa daga Dutsen Lebanon.
16 Farka, ya iskar arewa.
Ki hura a kan lambuna, ke iskar kudu.
Iska ta cika da ƙanshi.
Bari ƙaunataccena ya zo lambunsa,
Ya ci ‘ya’yan itatuwa mafi kyau.