1 Na shiga cikin lambuna, budurwata, amaryata,
Ina tattara mur da ƙaro.
Ina shan zuma da kakinsa.
Ina shan ruwan inabi da madara kuma.
Ƙaunatattuna, ku ci ku sha, har ku bugu da ƙauna!
Shan Kewa
2 Ina barci, amma zuciyata na a farke,
Sai na ji ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa.
Buɗe mini in shigo, ƙaunatacciyata, budurwata, kurciyata,
Wadda ba wanda zai kushe ki.
Kaina ya jiƙe da raɓa,
Gashina ya yi danshi da laimar ƙāsashi.
3 Na riga na tuɓe tufafina, in sāke sa su kuma?
Na wanke ƙafafuna, in sāke ɓata su?
4 Ƙaunataccena ya janye hannunsa daga ƙofa,
Zuciyata kuwa tana kansa.
5 Sai na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena, ya shigo.
Hannuna sharkaf da mur,
Yatsuna suna ɗiga da mur sa’ad da na kama hannun ƙofar.
6 Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, amma ya riga ya tafi!
Na so in ji muryarsa ƙwarai!
Na neme shi, amma ban same shi ba.
Na yi kiransa, amma ba amsa.
7 Matsara masu kai da kawowa cikin birni suka same ni,
Suka doke ni suka yi mini rauni.
Matsaran da suke kan garu suka fige gyalena.
8 Ku yi mini alkawari ku matan Urushalima,
Idan kun ga ƙaunataccena,
Ku faɗa masa na yi suwu saboda ƙauna.
9 Ke mafi kyau cikin mata,
Ki faɗi yadda ƙaunatacce naki yake.
Wane abin sha’awa take gare shi,
Har da za mu yi miki alkawari?
Amarya Ta Yabi Ango
10 Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma,
Da ƙyar a sami ɗaya irinsa a cikin dubu goma.
11 Gashin kansa dogaye ne suna zarya,
Baƙi wulik kamar jikin shaya.
Kansa ya fi zinariya daraja.
12 Idanunsa kamar na kurciyoyi a bakin ƙorama,
Waɗanda suka yi wanka da madara suna tsaye a bakin rafi.
13 Kumatunsa kyawawa ne kamar lambu,
Wanda yake cike da tsire-tsire da kayan yaji.
Leɓunansa kamar furen bi-rana ne, suna bulbulo da mur.
14 Hannuwansa kyawawa ne,
Saye da ƙawanen da aka yi musu ado da duwatsu masu daraja.
Ƙugu nasa sumul sumul ne kamar hauren giwa da aka manne da yakutu.
15 Cinyoyinsa kamar ginshiƙan da aka yi da dutsen alabasta,
Aka kafa su a cikin kwasfar zinariya.
Kamanninsa kamar Dutsen Lebanon ne,
Da itatuwan al’ul ɗinsa mafi kyau.
16 Bakinsa yana da daɗin sumbata,
Kome nasa yana faranta mini rai.
Matan Urushalima, yadda ƙaunataccena yake ke nan.