1 Ke mafi kyau cikin matan,
Ina ƙaunatacce naki ya tafi?
Wace hanya ƙaunatacce naki ya bi?
Za mu taimake ki nemansa.
2 Ƙaunataccena ya tafi lambunsa inda fangulan furanninsa suke.
Yana kiwon garkensa a lambun, yana tattara furannin bi-rana.
3 Ƙaunataccena nawa ne, ni kuma tasa ce,
Yana kiwon garkensa a cikin bi-rana.
Ango Ya Yabi Amarya
4 Ƙaunatacciyata, kina kyakkyawa kamar Urushalima,
Kyakkyawa kuma kamar birnin Tirza,
Kina da shiga rai kamar ɗaya daga cikin biranen nan.
5 Ki daina dubana gama idanunki suna rinjayata,
Gashinki yana zarya kamar garken awaki
Da yake gangarowa daga tuddan Gileyad.
6 Haƙoranki farare fat kamar tunkiyar da aka yi mata sausaya
Aka yi mata wanka nan da nan.
Ba giɓi, suna nan shar.
An jera su tantsai.
7 Kumatunki suna haske bayan lulluɓi.
8 Ina da matan aure sittin, kowace kuwa sarauniya ce,
Da ƙwaraƙwarai tamanin, da ‘yan mata kuwa ba a magana!
9 Amma ɗaya kaɗai nake ƙauna,
Ita kyakkyawa ce kamar kurciya.
Tilo ce ga mahaifiyarta, ‘yar lele ce ga mahaifiyarta.
Mata duk sukan dube ta, su yaba.
Matan sarki da ƙwaraƙwaransa suka raira waƙa suka yabe ta.
10 Wace ce wannan, kamar ketowar alfijir?
Ita kyakkyawa ce mai haske, kamar hasken rana,
Ko na wata mai kashe ido.
11 Na gangara zuwa cikin itatuwan almond
Domin in ga ƙananan itatuwan da suke a kwarin,
Domin in ga ganyayen inabi
Da furannin itatuwan rumman.
12 Ina karkaɗuwa, don kin sa in ƙosa saboda ƙauna,
Kamar mai korar dawakan karusar yaƙi.
13 Komo, ki komo, ke Bashulamiya,
Ki komo, ki komo domin mu ƙara dubanki.
Me ya sa kuke so ku dubi Bashulamiya,
Sa’ad da take taka rawar zamanin dā?