1 Da ma a ce kai ɗan’uwana ne, wanda mahaifiyata ta goya,
Da in na gamu da kai a titi,
Sai in sumbace ka, ba wanda zai kula.
2 Sai in kai ka gidan mahaifiyata,
In ba ka gaurayayyen ruwan inabina wanda aka yi da rumman, ka sha.
3 In ta da kai da hannun hagunka,
Ka rungume ni da hannun damanka.
4 Ku yi mini alkawari, ku matan Urushalima,
Ba za ku shiga tsakaninmu ba.
Ƙauna Tana da Iko kamar Mutuwa
5 Wace ce take zuwa daga cikin jeji,
Kafaɗa da kafaɗa da ƙaunataccenta?
A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke,
A wurin da aka haife ki,
Wurin da mahaifiyarki ta haife ki.
6 Kada ki ƙaunaci kowa sai ni,
Kada ki rungume kowa sai ni.
Ikon ƙauna kamar na mutuwa ne,
Ƙarfin kishin ƙauna kamar na mutuwa ne.
Yakan kama kamar wuta,
Yakan ci kamar gagarumar wuta.
7 Kome yawan ruwa ba zai iya kashe ta ba.
Ba rigyawar da za ta nutsar da ita.
Duk wanda ya ce zai iya sayen ƙauna da dukiya,
Ba abin da zai same shi sai tashin hankali.
8 Muna da ‘yar’uwa ƙunƙuma.
Me za mu yi idan wani saurayi ya ce yana sonta?
9 Da a ce ita bango ce, da mun gina mata hasumiyar azurfa.
Da a ce ita ƙofa ce, da mun yi mata ƙyaure da itacen al’ul.
10 Ni bango ce, doguwa, mamana tantsai tantsai,
Na sami kwarjini wurin ƙaunataccena.
11 Sulemanu yana da gonar inabi
A Ba’al-hamon, wato wuri mai yawan albarka.
Ya yi ijara da waɗansu zaɓaɓɓun manoma.
Kowannensu yana biyansa kuɗi, azurfa dubu.
12 Ni ma ina da gonar inabi ta kaina.
Kai Sulemanu zan ba ka kuɗi azurfa dubu,
Sauran ma’aikata kuma zan ba kowanne ɗari biyu.
13 Aminaina suna kasa kunne ga ƙaunataccena.
Ina so in ji muryarka daga cikin lambun.
14 Ya ƙaunataccena, ka zo wurina da sauri, kamar batsiya,
Ko sagarin kishimi a kan duwatsu inda kayan yaji yake tsirowa.