Shaidu Biyu Ɗin
1 Sa’an nan aka ba ni wata gora kamar sanda, aka kuma ce mini, “Tashi ka auna Haikalin Allah, da bagadin hadaya, da kuma masu sujada a ciki,
2 amma kada ka auna harabar Haikalin, ka ƙyale ta, domin an ba da ita ga al’ummai, za su tattake tsattsarkan birnin nan har wata arba’in da biyu.
3 Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi annabci kwana dubu da metan da sittin, suna a saye da tsummoki.”
4 Waɗannan su ne itatuwan zaitun ɗin nan guda biyu, da fitilun nan biyu da suke a tsaye a gaban Ubangijin duniya.
5 In kuwa wani yana da niyyar cutarsu, sai wuta ta huro daga bakinsu, ta lashe maƙiyansu, duk mai niyyar cutarsu kuwa, ta haka ne lalle za a kashe shi.
6 Suna da ikon hana ruwan sama, don kada a yi ruwa a duk kwanakin da suke yin annabci, suna kuma da iko a kan ruwa, su mai da shi jini, su kuma ɗora wa duniya kowane irin bala’i, a duk lokacin da suke so.
7 Bayan da suka ƙare shaidarsu, sai wata dabba mai fitowa daga mahallaka tă yaƙe su, ta cinye su, ta kashe su,
8 a kuma bar gawawwakinsu a kan hanyar babban birnin nan da ake kira Saduma da Masar ga ma’ana ta ruhu, a inda aka gicciye Ubangijinsu.
9 Mutanen dukkan jama’a, da kabila, da harshe, da al’umma za su riƙa kallon gawawwakinsu, har kwana uku da rabi, su kuwa ƙi yarda a binne su.
10 Mazaunan duniya kuma, sai su yi ta alwashi a kansu, suna ta shagali, suna a’aika wa juna da kyauta, domin annabawan nan biyu dā sun azabtar da mazaunan duniya.
11 Amma bayan kwana uku da rabin nan, sai numfashin rai daga wurin Allah ya shiga a cikinsu, suka tashi a tsaye, matsanancin tsoro kuwa ya rufe waɗanda suka gan su.
12 Sai suka ji wata murya mai ƙara daga sama tana ce musu, “Ku hawo nan!” Sai suka tafi sama a cikin gajimare, maƙiyansu suna gani.
13 A nan tāke sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, sai ushirin garin ya zube, mutum dubu bakwai aka kashe a rawar ƙasar, sauran kuwa suka tsorata, suka ɗaukaka Allah Mai Sama.
14 Bala’i na biyu ya wuce, ga kuma bala’i na uku yana zuwa nan da nan.
Ƙaho na Bakwai
15 Sa’an nan mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”
16 Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke a zaune a kan kursiyansu a gaban Allah suka fādi suka yi wa Allah sujada,
17 Suna cewa,
“Mun gode maka, ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki,
Wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā,
Saboda ka ɗauki ikonka mai girma, kana mulki.
18 Al’ummai sun husata, fushinka kuwa ya auko,
Lokaci ya yi da za a yi wa matuttu shari’a,
A kuma yi wa bayinka, annabawa da tsarkaka sakamako,
Da masu jin tsoron sunanka, yaro da babba,
A kuma hallaka masu hallaka duniya.”
19 Sa’an nan aka buɗe Haikalin nan na Allah da yake a Sama, aka kuma ga akwatin alkawarinsa a Haikalinsa. Sai aka yi ta walƙiya da kururuwa, da aradu, da rawar ƙasa, da ƙanƙara manya manya.