Wata Mace da Macijin
1 Aka kuma ga wata babbar alama a sama, wata mace tana a lulluɓe da rana, tana a tsaye a kan wata, da kuma kambi mai taurari goma sha biyu a kanta.
2 Tana da ciki, sai kuma ta yi ta ƙara ta ƙagauta domin ta haihu, saboda azabar naƙuda.
3 Sai kuma aka ga wata alama a sama, ga wani ƙaton jan maciji mai kawuna bakwai, da ƙahoni goma, da kambi bakwai a kawunansa.
4 Wutsiyarsa ta sharo sulusin taurari, ta zuba su a ƙasa. Sai macijin ya tsaya a gaban matar nan mai naƙuda, don ya lanƙwame ɗan nata in ta haife shi.
5 Ta kuwa haifi ɗa namiji, wanda zai mallaki dukkan al’ummai da sandar ƙarfe, amma aka fyauce ɗan nata, aka kai shi zuwa wurin Allah da kursiyinsa.
6 Matar kuwa, sai ta gudu ta shiga jeji, a inda Allah ya shirya mata wurin da za a cishe ta har kwana dubu da metan da sittin.
7 Sai yaƙi ya tashi a sama, Mika’ilu da mala’ikunsa suna yaƙi da macijin nan, macijin kuma da mala’ikunsa suka yi ta yaƙi,
8 amma aka cinye su, har suka rasa wuri a sama sam.
9 Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala’ikunsa ma aka jefa su tare da shi.
10 Sai na ji wata murya mai ƙara a Sama tana cewa, “A yanzu fa, ceto, da ƙarfi, da mulki na Allahnmu, da kuma ikon Almasihunsa sun bayyana, don an jefa mai ƙarar ‘yan’uwanmu a ƙasa, shi da yake ƙararsu dare da rana a gun Allahnmu.
11 Sun kuwa yi nasara da shi albarkacin jinin Ɗan Ragon nan, da kuma albarkacin maganar da suka shaida, domin ba su yi tattalin ransu ba, har abin ya kai su ga kisa.
12 Saboda haka, sai ku yi farin ciki, ya ku sammai, da ku mazauna a ciki. Amma kaitonku, ke ƙasa, da kai teku, don Ibilis ya sauko gare ku da matsanancin fushi, don ya san lokacinsa ya ƙure.”
13 Da macijin nan ya ga an jefa shi a ƙasa, ya fafari matar nan da ta haifi ɗa namiji, da tsanani.
14 Amma aka ba matar fikafikan nan biyu na babban juhurman nan, don ta tashi ta guje wa macijin nan, ta shiga jeji, ta je wurin da za a cishe ta a lokaci ɗaya, da lokatai, da rabin lokaci.
15 Sai macijin ya kwarara ruwa daga bakinsa kamar kogi daga bayan matar, don ya share ta da ambaliya.
16 Amma ƙasa ta taimaki matar, ita ƙasar ta buɗe bakinta ta shanye kogin da macijin nan ya kwararo daga bakinsa.
17 Macijin kuwa ya yi fushi da matar, ya tafi ya ɗaura yaƙi da sauran zuriyarta, wato, waɗanda suke kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu. Sai ya tsaya a kan yashin teku.