Waƙar 144,000 Ɗin
1 Sa’an nan na duba, sai ga Ɗan Ragon nan a tsaye a kan Dutsen Sihiyona, akwai kuma mutum dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu tare da shi, waɗanda aka rubuta sunansa, da sunan Ubansa, a goshinsu.
2 Sai na ji wata murya daga Sama kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, muryar da na ji kuwa, kamar ta masu molo ce na kiɗan molo.
3 Suna raira wata sabuwar waƙa a gaban kursiyin, a gaban rayayyun halittan nan huɗu, da kuma a gaban dattawan nan. Ba mai iya koyon waƙar nan, sai mutum dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu ɗin nan, waɗanda aka fanso daga duniya.
4 Waɗannan su ne waɗanda ba su taɓa ƙazantuwa da fasikanci ba, domin su tsarkaka ne. Su ne kuma suke bin Ɗan Ragon a duk inda ya je. Su ne kuma aka fanso daga cikin mutane a kan su ne nunan fari na Allah, da na Ɗan Ragon nan kuma,
5 ba wata ƙarya a bakinsu, domin su marasa aibu ne.
Sanarwar Mala’iku Uku Ɗin
6 Sa’an nan na ga wani mala’ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar bishara, domin ya sanar da ita ga mazaunan duniya, wato, ga kowace al’umma, da kabila, da harshe, da jama’a.
7 Sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi, domin lokacinsa na yin hukunci ya yi. Ku yi masa sujada, shi da ya halicci sama, da ƙasa, da teku, da kuma maɓuɓɓugan ruwa.”
8 Sai kuma mala’ika na biyu ya biyo, yana cewa, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ita da ta zuga dukkan al’ummai su yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita.”
9 Sai kuma mala’ika na uku ya biyo, yana ɗaga murya da ƙarfi, yana cewa, “Duk mai yi wa dabbar nan da siffarta sujada, wanda kuma ya yarda a yi masa alama a goshinsa, ko a hannunsa,
10 zai ci karo da azabar Allah tsantsa ta tsananin fushinsa, za a kuwa azabta shi da wuta, da duwatsun wuta, a gaban mala’iku tsarkaka, da kuma Ɗan Ragon.
11 Hayaƙin azabar nan tasu ya dinga tashi har abada abadin, ba su da wani rangwame dare da rana, wato, waɗannan masu yi wa dabbar nan da siffarta sujada, da kuma duk wanda ya yarda aka yi masa alamar sunanta.”
12 Wannan yana nuna jimirin tsarkaka, masu kiyaye umarnin Allah da kuma bangaskiya ga Yesu.
13 Sai kuma na ji wata murya daga Sama tana cewa, “Rubuta wannan. Albarka tā tabbata ga matattu, wato, waɗanda za su mutu a nan gaba a kan su na Ubangiji ne.” Ruhu ya ce, “Hakika, masu albarka ne, domin su huta daga wahalarsu, gama aikinsu yana a biye da su!”
Girbe Duniya
14 Sa’an nan na duba, sai ga wani farin gajimare, da wani kamar Ɗan Mutum a zaune a kan gajimaren, da kambin zinariya a kansa, da kakkaifan lauje a hannunsa.
15 Sai mala’ika ya fito daga Haikalin, yana magana da murya mai ƙarfi da wanda yake a zaune a kan gajimaren, yana cewa, “Ka sa laujenka ka yanke, don lokacin yanka ya yi, amfanin duniya ya nuna sarai.”
16 Sai wanda yake a zaune a kan gajimaren ya wurga laujensa zuwa duniya, aka girbe amfanin duniya.
17 Wani mala’ika kuma ya fito daga Haikali a Sama, shi ma kuwa yana da kakkaifan lauje.
18 Sai kuma wani mala’ika ya fito daga bagadin ƙona turare, wato, mala’ikan da yake da iko da wutar, ya yi magana da murya mai ƙarfi da wannan mai kakkaifan lauje, ya ce, “Ka sa laujenka ka yanke nonnan inabin zuwa duniya, don inabin ya nuna.”
19 Sai mala’ikan ya wurga laujensa duniya, ya tattara inabin duniya, ya zuba a cikin babbar mamatsar inabi ta fushin Allah.
20 Aka tattake mamatsar inabin a bayan gari, jini kuma ya yi ta gudana daga mamatsar inabin, ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, har mil metan.