Faɗuwar Babila Mai Girma
1 Bayan haka, na ga wani mala’ika yana saukowa daga Sama, mai iko da yawa, sai aka haskaka duniya da ɗaukakarsa.
2 Sai ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ce,
“Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi!
Ta zama mazaunin aljannu,
Matattarar kowane baƙin aljani,
Da kowane irin ƙazamin tsuntsu, abin ƙyama.
3 Dukkan al’ummai sun yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita,
Sarakunan duniya kuma sun yi fasikanci da ita,
Attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”
4 Sai na ji wata murya daga Sama, tana cewa,
“Ku fito daga cikinta, ya ku jama’ata,
Kada zunubanta su shafe ku,
Kada bala’inta ya taɓa ku.
5 Domin zunubanta sun yi tsororuwa, sun kai har Sama,
Allah kuwa ya tuna da laifofinta.
6 Ku saka mata daidai da yadda ta yi,
Ku biya ta ninkin ayyukanta,
Ku dama mata biyun abin da ta dama muku.
7 Yadda ta ɗaukaka kanta, ta yi almubazzaranci,
Haka ku ma ku saka mata da azaba, da baƙin ciki gwargwadon haka.
Tun da yake a birnin zuciyarta ta ce, ‘Ni sarauniya ce, a zaune nake,
Ni ba gwauruwa ba ce,
Ba ni da baƙin ciki kuma har abada!’
8 Saboda haka, bala’inta zai aukar mata rana ɗaya,
Mutuwa, da baƙin ciki, da yunwa.
Za a kuma ƙone ta,
Domin Ubangiji Allah da yake hukunta ta Mai Ƙarfi ne.”
9 Sarakunan duniya kuma da suka yi fasikanci da zaman almubazzaranci da ita, za su yi mata kuka da kururuwa, in sun ga hayaƙin ƙunarta,
10 za su tsaya a can nesa, don tsoron azabarta, su ce,
“Kaitonka! Kaitonka, ya kai babban birni!
Ya kai birni mai ƙarfi, Babila!
A sa’a ɗaya hukuncinka ya auko.”
11 Attajiran duniya kuma suna yi mata kuka suna baƙin ciki, tun da yake, ba mai ƙara sayen kayansu,
12 wato, zinariya, da azurfa, da duwatsun alfarma, da lu’ulu’u, da lallausan lilin, da hajja mai ruwan jar garura, da siliki, da jan alharini, da itacen ƙanshi iri iri, da kayan hauren giwa iri iri, da kayan da aka sassaƙa da itace mai tsada, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na dutse mai sheƙi,
13 da kirfa, da kayan yaji, da turaren wuta, da mur, da lubban, da ruwan inabi, da mai, da garin alkama, da alkama, da shanu, da tumaki, da dawaki, da kekunan doki, da kuma bayi, wato, rayukan ‘yan adam.
14 “Amfanin da kika ƙwallafa rai a kai, har ya kuɓuce miki,
Kayan annashuwarki da na adonki sun ɓace miki, ba kuwa za a ƙara samunsu ba har abada!”
15 Attajiran waɗannan hajjoji da suka arzuta a game da ita, za su tsaya a can nesa don tsoron azabarta, suna kuka, suna baƙin ciki, suna cewa,
16 “Kaito! Kaiton babban birnin nan!
Wanda dā ya sa lallausan lilin, da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma jan alharini,
Wanda ya ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu’ulu’u!
17 Domin a sa’a ɗaya duk ɗumbun dukiyar nan ta hallaka.”
Sai duk masu jiragen ruwa, da masu shiga, da masu tuƙi, da duk waɗanda cinikinsu ya gamu da bahar, suka tsaya a can nesa,
18 suna kururuwa da suka ga hayaƙin ƙunarsa, suna cewa,
“Wane birni ne ya yi kama da babban birnin nan?”
19 Har suka tula wa kansu ƙasa suna ta kuka, suna baƙin ciki, suna kururuwa, suna cewa,
“Kaito! Kaiton babban birnin nan!
Wanda duk masu jiragen ruwa a bahar suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa,
A sa’a ɗaya ya hallaka.
20 Ki yi farin ciki saboda an yi masa haka, ya sama!
Ku yi farin ciki, ku tsarkaka da manzanni da annabawa, domin Allah ya rama muku abin da ya yi muku!”
21 Sai wani ƙaƙƙarfan mala’ika ya ɗauki wani dutse kamar babban dutsen niƙa, ya jefa a teku, ya ce,
“Haka za a fyaɗa Babila babban birni, da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.
22 Ba za a ƙara jin kiɗan masu molo, da mawaƙa, da masu sarewa, da masu bushe-bushe a cikinki ba,
Ba kuma za a ƙara ganin mai kowace irin sana’a a cikinki ba,
Ba kuma za a ƙara jin niƙa a cikinki ba,
23 Fitila ba za ta ƙara haskakawa a cikinki ba,
Ba kuma za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba,
Don attajiranki, dā su ne ƙusoshin duniya,
An kuma yaudari dukkan al’ummai da sihirinki.
24 Har an tarar hakkin jinin annabawa da na tsarkaka suna a wuyanta, da kuma na duk waɗanda aka kashe a duniya.”