Saƙo Zuwa ga Sardisu
1 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Sardisu haka, ‘Ga maganar mai Ruhohin Allah guda bakwai, da kuma taurarin nan bakwai.
“ ‘Na san ayyukanka, kai rayayye ne, alhali kuwa matacce ne kai.
2 Ka yi zaman tsaro, ka ƙarfafa abin nan da ya saura, yake kuma a bakin mutuwa, don ban ga aikinka cikakke ne ba a gaban Allahna.
3 Don haka, sai ka tuna da abin da ka karɓa ka kuma ji, ka kiyaye shi, sa’an nan ka tuba. In ba za ka yi tsaro ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san a lokacin da zan auko maka ba.
4 Amma dai har yanzu kana da waɗansu kaɗan a Sardisu da ba su ƙazantar da kansu ba, za su kuwa kasance tare da ni da fararen kaya, don sun cancanta.
5 Duk wanda ya ci nasara, za a sa masa fararen tufafi, ba kuwa zan soke sunansa daga Littafin Rai ba, zan ce shi nawa ne a gaban Ubana, da kuma a gaban mala’ikunsa.
6 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”
Saƙo Zuwa ga Filadalfiya
7 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Filadalfiya haka, ‘Ga maganar Mai Tsarkin nan, Mai gaskiya, wanda yake da mabuɗin Dawuda, wanda in ya buɗe, ba mai rufewa, in kuma ya rufe, ba mai buɗewa.
8 “ ‘Na san ayyukanka. Ka ga, na bar maka ƙofa a buɗe, wadda ba mai iya rufewa. Na dai san ƙarfinka kaɗan ne, duk da haka, kā kiyaye maganata, ba ka yi musun sanin sunana ba.
9 To, ga shi, zan sa su waɗanda suke daga jama’ar Shaiɗan, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, ƙarya suke yi, zan sa su, su zo, su kwanta a gabanka, su sani dai na ƙaunace ka.
10 Tun da yake ka kiyaye maganar da na yi maka ta yin jimiri, Ni ma zan kiyaye ka daga sharrin lokacin nan na gwaji, wanda zai auko wa dukan duniya, don a gwada mazaunan duniya.
11 Ina zuwa da wuri. Ka riƙi abin da kake da shi kankan, kada wani ya karɓe maka kambinka.
12 Duk wanda ya ci nasara, zan mai da shi ginshiƙi a Haikalin Allahna. Ba zai ƙara fita daga ciki ba, zan kuma rubuta sunan Allahna a jikinsa, da sunan Birnin Allahna, wato, Sabuwar Urushalima, mai saukowa daga wurin Allahna daga Sama, da kuma nawa sabon suna.
13 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”
Saƙo Zuwa ga Lawudikiya
14 “Ka kuma rubuta wa mala’ikan ikkilisiyar da take a Lawudikiya haka, ‘Ga maganar tabbataccen nan, Amintaccen Mashaidi mai gaskiya, wanda ta wurinsa dukkan halittar Allah ta kasance.
15 “ ‘Na san ayyukanka. Ba ka da sanyi, ba ka kuwa da zafi. Da ma a ce kana da sanyi, ko kuwa kana da zafi.
16 To, saboda kai tsakatsaki ne, ba ka da sanyi, ba ka kuwa da zafi, zan tofar da kai daga bakina.
17 Tun da ka ce, kai mai arziki ne, cewa ka wadata ba ka bukatar kome, ba ka sani ba kuwa kai ne matsiyacin, abin yi wa kaito, matalauci, makaho, tsirara kuma.
18 Saboda haka, ina yi maka shawara ka sayi zinariya a guna, wadda aka tace da wuta, don ka arzuta, da kuma fararen tufafi da za ka yi sutura, ka rufe tsiraicinka don kada ka ji kunya, da kuma man shafawa a ido don ka sami gani.
19 Waɗanda nake ƙauna, su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka, sai ka himmantu ka tuba.
20 Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni.
21 Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin zama tare da ni a kursiyina. kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a kursiyinsa.
22 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”