Yimƙaƙƙen Littafin da Ɗan Ragon
1 A hannun dama na wanda yake zaune a kursiyin kuma, sai na ga wani littafi rubutacce ciki da bai, an yimƙe shi da hatimi bakwai.
2 Na kuma ga wani ƙaƙƙarfan mala’ika, yana shela da murya mai ƙarfi cewa, “Wa ya cancanta ya buɗe littafin nan, ya kuma ɓamɓare hatimansa?”
3 Ba kuwa wani a Sama ko a ƙasa, ko a ƙarƙashin ƙasa, da zai iya buɗe littafin, balle yă duba a cikinsa.
4 Sai na yi ta kuka da ba a sami wanda ya cancanta ya buɗe littafin, ko ya duba a cikinsa ba, ko ɗaya.
5 Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya ce mini, “Kada ka yi kuka. Ga shi, Zakin nan na kabilar Yahuza, Tsatson Dawuda, ya ci nasara har yake da iko yă buɗe littafin nan da hatimansa bakwai.”
6 Sai na ga wani Ɗan Rago yana a tsaye a tsakiyar kursiyin, kewaye da shi kuma ga rayayyun halittan nan huɗu da dattawan, Ɗan Ragon kuwa kamar yankakke ne, yana da ƙaho bakwai da ido bakwai, waɗanda suke Ruhohin Allah guda bakwai, da aka aika a duniya duka.
7 Sai ya je ya ɗauki littafin nan daga hannun dama na wanda yake a zaune a kan kursiyin.
8 Da ya ɗauki littafin, rayayyun halittan nan guda huɗu, da dattawan nan ashirin da huɗu, suka fāɗi gaban Ɗan Ragon, kowannensu yana riƙe da molo, da tasar zinariya a cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka.
9 Suna raira sabuwar waƙa, suna cewa,
“Macancanci ne kai ka ɗauki littafin nan, ka ɓamɓare hatimansa,
Domin dā an kashe ka, ka kuma fanso wa Allah mutane ta jininka
Daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama’a, da kowace al’umma,
10 Ka mai da su firistoci mallakar Allahnmu, za su kuwa mallaki duniya.”
11 Sa’an nan na duba, sai na ji muryar mala’iku masu yawa, a kewaye da kursiyin, da rayayyun halittan nan, da kuma dattawan nan, yawansu zambar dubu har dubun dubbai,
12 suna cewa da murya mai ƙarfi, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka yanka yă sami iko, da wadata, da hikima, da ƙarfi, da girma, da ɗaukaka, da yabo!”
13 Sai na ji kowace halittar da take a Sama, da ƙasa, da ƙarƙashin ƙasa, da bisa teku, da kuma dukkan abin da yake cikinsu, suna cewa, “Yabo, da girma, da ɗaukaka, da mulki sun tabbata ga wanda yake a zaune a kan kursiyin, da Ɗan Ragon nan, har abada abadin!”
14 Sai rayayyun halittan nan huɗu suka ce, “Amin! Amin!” Dattawan nan kuma suka fāɗi suka yi sujada.